Buhari ga ƴan Najeriya: Nima Ina jin Irin Keburan da Kuke Sha

Buhari ga ƴan Najeriya: Nima Ina jin Irin Keburan da Kuke Sha

  • Buhari ya yi bayani game da irin yadda yake ji kan matsalolin da suka addabi daukacin yan Najeriya
  • Sannan ya bayyana cewa ya cika alƙawura da ya yi a shekarun 2015 da 2019 a yayin yaƙin neman zaɓensa
  • Tare da tabbatar da yadda gwamnatinsa ta yi nasarar magance matsalar tsaro a Najeriya

Abuja - A yayin da kwanaki kaɗan ya rage wa shugaba Buhari ya yi bankwana da kujerarsa da ya shafe shekaru takwas yana juyawa a kanta, ya tabbatar wa da ƴan Najeriya cewa, haƙurinsu da juriyarsu ba zai tafi a banza ba.

Buhari ya fara da bayyana cewa, a yayin da gwamnatinsa ke cin ƙarfin matsalar tsaro, sai kuma aka samu ɓullar wani nau’i na matsalar tsaron da ba a san da shi ba kamar garkuwa da mutane, kisan kiyashi da ayyukan ta’addanci waɗanda kuma jam’ina tsaro ke cigaba da namijin ƙoƙari wajen magance su.

Kara karanta wannan

Ku Shiga Harkokin Siyasar 2023 Ayi Da Ku, Buhari Ya Buƙaci Mata da Matasa

Buhari
Buhari ga ƴan Najeriya: Nima Ina jin Irin Keburan da Kuke Sha Hoto: Buhari
Asali: Depositphotos

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a jawabin murnar cikar Najeriya shekaru 62 da samu yancin kai daga wajen turawan mulkin mallaka, rahoton ChannelsTV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar:

“Ina jin irin yadda kuke ji kuma ina mai tabbatar muku cewa za ku ci ribar haƙurinku da juriyarku, domin muna cigaba da bunƙasa fannin tsaro wajen ganin sun magance matsalar tsaro,”
“Mun yi nasara a ɓangaren tattalin arziƙi da tsaro tun bayan shigarmu ofis a watan Mayun 2015 a lokacin da na yi alƙawarin bunƙasa tattalin arziƙi da magance cin-hanci da rashawa da kuma ƙara yin alƙawarin yaye wa mutane miliyan ɗari talauci na tsawon shekaru goma kamar yadda muka shirya da babban bankin Najeriya (CBN) a yayin yaƙin neman zaɓen 2019.”

Kalli bidiyon:

Buhari Ya Buƙaci Mata da Matasa Su Shiga Harkokin Siyasa a 2023

Kara karanta wannan

Tinubu Na Nan Lafiya Lau A Landan, In Ji Kakakin Kamfen APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci mata da matasa su ƙara shiga harkokin siyasa ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba, 2022.

Shugaban ya buƙaci matasa da su kaucewa shiga duk wani abu na tarzoma.

Sannan shugaban ya yi kira ga ƴan siyasa da su kaucewa zantuka na ɓatanci ga juna da kuma fatan cewa za su mai da hankali ga yin kanfen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel