Buhari Ya Buƙaci Mata da Matasa Su Shiga Harkokin Siyasa a 2023

Buhari Ya Buƙaci Mata da Matasa Su Shiga Harkokin Siyasa a 2023

  • Shugaba Buhari ya bayyana burinsa na ganin mata da matasa sun shiga harkokin zaɓen 2023
  • Sannan ya buƙaci matasan da su kaucewa shiga duk wani abu da zai haifar da tashin hankali da tarzoma
  • Buharin ya bayyana irin cigaban da gwamnatinsa ta samu da kowa ke iya gani a ƙasa ba sai an bada labari ba

Abuja -Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci mata da matasa su ƙara shiga harkokin siyasa ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba, 2022.

Shugaban ya buƙaci matasa da su kaucewa shiga duk wani abu na tarzoma, rahoton ChannelsTV.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a jawabin murnar cikar Najeriya shekaru 62 da samu yancin kai daga wajen turawan mulkin mallaka.

A cewarsa;

“ina mai fatan ganin ƙaruwar mata da matasa a harkokin zaɓe da ke ƙaratowa. Kuma ina da tabbacin cewa matasamu masu jini a jika za su kaucewa shiga kowacce iriyar tarzoma domin kaucewa zama yaran ƴan siyasa domin cimma manufarsu.”

Kara karanta wannan

Buhari ga ƴan Najeriya: Nima Ina jin Irin Keburan da Kuke Sha

Buhari
Buhari Ya Buƙaci Mata da Matasa Su Shiga Harkokin Siyasa a 2023 Hoto: Presidency
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sannan shugaban ya yi kira ga ƴan siyasa da su kaucewa zantuka na ɓatanci ga juna da kuma fatan cewa za su mai da hankali ga yin kanfen.

Har’ila yau, shugaban ya shawararci al’umma da su buƙaci masu neman muƙamai da wajen yin ayyuka na cigaban ƙasa.

Ya kara da cewa:

“Sannan muna cigaba da haɗa kai da sauran ƙasashe a duk lokacin da buƙatar hakan ta tasu domin ciyar da Najeriya gaba,”
“A shekarun da suka wuce, ƴan Najeriya shaidu ga irin ƙalubalen da muka fuskanta waɗanda suka kusa runguza mana ƙasa. Da irin wannan ƙarfin guiwa tamu nake fatan za mu haɗa kai domin samun nasara gaba ɗaya kamar yadda ni ma na samu damar yin jagoranci da kuma kafa tuwasun samar da cigaban wannan ƙasa.

Kara karanta wannan

Nigeria @62: 'Yan Najeriya Sun Gaji Da Shugabannni Gajiyayyu masu gajiyawa, Peter Obi

Tinubu Ya Nada Uwargidar Shugaba Buhari Matsayin Jagorar Mata A Kamfensa, Ba Sunan Matar Osinbajo

Jam’iyya mai mulki a Nijeriya ta APC, ta sanar da nada Matar shugaban kasa Aisha Buhari a matsayin wadda zata jagoranci mata a kamfen din jami’iyyar na 2023, a yau asabar.

Sauran wadanda zasu taka rawa a tawagar sun hada da Sanata Oluremi Tinubu, Sanata mai wakiltan Legas ta tsakiya a zauren majalisar dattawa a wa'adi na uku a majalisar dattawa kuma tsohuwar uwargidan tsohon gwamnan jihar Legas, Nana Shettima, tsohuwar uwargidan gwamnan jihar Borno kuma uwargidan dan takarar mataimakin shugaban kasa jam'iyyar APC.

Tawagar dai zasu yi aiki ne a matsayin Shugaba da Mataimakan Shugabanin tawagar kamfe a bangaren mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel