Firai Ministan Girka Ya Gayyaci Buhari Kasarsa Kan Wa'adinsa Ya Kare

Firai Ministan Girka Ya Gayyaci Buhari Kasarsa Kan Wa'adinsa Ya Kare

  • Shugaba Buhari ya samu goron gayyata ta musamman daga Firai Ministan Girka, Kyriakos Mitsotakis
  • Kyriakos Mitsotakis yace shugaba Buhari ya zo kasarsa kafin wa'adinsa ya kare a Mayun 2023
  • Buhari da gomman mukarrabansa na kasar Amurka don halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya

Amurka - Shugaba Muhammadu Buhari ya zanna da Firai Ministan Girka, Kyriakos Mitsotakis, a New York, hedkwatar majalisar dinkin duniya dake kasar Amurka.

Buhari ya yi kira ga Firai Ministan ya karfafa alaka da Najeriya ta bangaren ilimi, kiwon lafiya, da tsaro.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar ranar Asabar, yace Buhari ya jaddadawa Firai Ministan muhimmancin ilimi kuma lokaci ya yi.

Buhari
Firai Ministan Girka Ya Gayyaci Buhari Kasarsa Kan Wa'adinsa Ya Kare
Asali: Facebook

Firai Ministan Girka a jawabinsa yace kasarsa na da fasahohin zamani da zasu taimakawa Najeriya wajen magance matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Nan Ba Da Dadewa Ba Matsalar Tsaro Zai Zama Tarihi , Shugaba Buhari Ya Yi Alkawari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adesina ya ruwaito shi da cewa:

"Girka na da ilimin fasahar tsaro, leken asiri, da amfani da bayanan sirri kuma zamu iya taimakon Najeriya."
"Duk da cewa fasahohin na da tsada, shine hanya mafi dadewa saboda babu wata hanyar samar da zaman lafiya."

Bayan haka, Firai Ministan ya gayyaci Shugaba Buhari kasarsa kafin wa'adin mulkinsa ya kare.

Matsalar Tsaro Zai Zama Tarihi Nan Ba Da Dadewa ba, Shugaba Buhari Ya Yiwa Yan Najeriya Alkawari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dubi da yadda dakarun sojin Najeriya suka kara kaimi wajen yakan yan bindiga, matsalar tsaro zai zama tarihi nan ba da dadewa ba.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne ranar Asabar a New York, birnin Amurka yayin zama da Firai Ministan kasar Ireland, Michel Martin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel