Matsalar Tsaro Zai Zama Tarihi Nan Ba Da Dadewa ba, Shugaba Buhari Ya Yiwa Yan Najeriya Alkawari

Matsalar Tsaro Zai Zama Tarihi Nan Ba Da Dadewa ba, Shugaba Buhari Ya Yiwa Yan Najeriya Alkawari

  • Shugaba Buhari ya bada karfin gwiwan cewa nan ba da dadewa ba za'a shawo kan matsalar tsaro
  • Buhari da gomman mukarrabansa na kasar Amurka don halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya
  • Buhari ya gabatar da nasa jawabin ga shugabannin duniya a taron ranar Laraba

Amurka - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dubi da yadda dakarun sojin Najeriya suka kara kaimi wajen yakan yan bindiga, matsalar tsaro zai zama tarihi nan ba da dadewa ba.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne ranar Asabar a New York, birnin Amurka yayin zama da Firai Ministan kasar Ireland, Michel Martin.

Buhari
Matsalar Tsaro Zai Zama Tarihi Nan Ba Da Dadewa ba, Shugaba Buhari Ya Yiwa Yan Najeriya Alkawari
Asali: Facebook

A jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar ranar Asabar, yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a a New York ya bayyana cewa bisa yadda Sojojin Najeriya ke kokari, matsalar tsaro zata zama tarihi."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Shugaba Buhari ya ce a watannin baya-bayan nan, kokarin da sojojin Najeriye keyi na nuna cewa muna hanyar shawo kan matsalar rashin tsaro."
"Zamu cigaba da had akai da kasashen duniya wajen amfani da fasaha saboda Najeriya ta amfana."

Adesina ya kara da cewa Firai Minista Mr Micheal Martin ya fadawa shugaba Buhari cewa kasar Ireland na neman hanyoyin karfafa alaka da Najeriya.

Ku Taimaka Ku Yafe Mana Basussukan Da Ake Binmu: Shugaba Buhari Ya Roki Shugabannin Duniya

A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da shugabannin kasashen duniya su yafewa Najeriya da kasashe masu tasowa basussukan da suke binsu saboda halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.

A jawabin da yayi a taron gangamin majalisar dinkin duniya ranar Laraba, Buhari yace kasashe masu tasowa na fuskantar kalubale da dama, cike har da rashin iya bisa basussuka.

Kara karanta wannan

Jakadan Kasar China Ya Yi Magana Kan Kwace Kadarorin Najeriya Idan Ta Gaza Biyan Bashi

Ya bukaci shugabannin duniya su taimaka su sanya baki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel