Da Yiwuwan El-Rufa'i Ya Dawo Ministan Abuja?: Hadimin Shugaba Buhari Yace Zai So Hakan

Da Yiwuwan El-Rufa'i Ya Dawo Ministan Abuja?: Hadimin Shugaba Buhari Yace Zai So Hakan

  • Shin mazauna birnin tarayya FCT Abuja zasu sake ganin dawowar Malam Nasir El-Rufa'i matsayin Minista
  • Hadimin shugaban Buhari ya bayyana cewa zai so a dawo da gwamnan Abuja bayan karewar wa'adinsa a Kaduna
  • Mutane sun bayyana mabanbantan ra'ayi kan wannan jawabi inda wasu ke tuna tarihi

FCT Abuja - Jama'a sun bayyana mabanbantan ra'ayi bayan hadimin shugaba Muhammadu Buhar, Bashir Ahmad, ya bayyana yiwuwar dawowar Gwamna Nasir El-Rufa'i na Kaduna matsayin Ministan Abuja.

A cewar jawabin da Bashir yayi a shafinsa na Tuwita da Legit.ng ta gani ranar Talata, yace ba zai yi mamaki ba Gwamnan ya dawo.

El-Rufa'i
Da Yiwuwan El-Rufa'i Ya Dawo Ministan Abuja: Hadimin Shugaba Buhari Yace Zai So Hakan
Asali: UGC

Yace:

"Ba zan yi mamaki ko ni kadai ne ba, amma ina addu'an ganin Nasir El-Rufa'i ya dawo Ministan birnin tarayya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

El-Rufa'i ya rike matsayin Ministan Abuja tsakanin 2003 da 2007 lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Mutane na bayyana cewa El-Rufa'i ya yi namijin kokarin lokacin da ya rike kujerar a baya.

Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu

Shoaib Nuhu Kankia

"Wlh muna so. Don a Life Camp kullum sai anyi kewar sa."

Zakariyya Gambo

"aiki sai mai shi muna murna da dawowarsa ABUJA tayi matsi ba iska mlm"

Cer Galadeemha

"Allah ubangiji ya tabbatar. The killer man"

Al Ameen Kurfi Jr.:

Tab zalunci sabo kenan
Mukam munsan da yadawo kwanan sunqare Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel