Ambaliyar Ruwa: Mutum 92 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Gwamna Ya Lula Yawon Shakawata Ketare

Ambaliyar Ruwa: Mutum 92 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Gwamna Ya Lula Yawon Shakawata Ketare

  • Mutum 92 sun sheka lahira sakamakon ambaliyar ruwa da ya ritsa da jama'a masu yawa a sassan jihar Jigawa
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamna ya lula kasar ketare domin hutawa kafin a fara gangamin zaben 2023
  • Jama'ar da lamarin ya ritsa da su sun koka kan yadda gwamnatin jihar tayi watsi da su tare da nuna halin ko in kula

Jigawa - Yawan wadanda ambaliyar ruwa yayi ajali a jihar Jigawa ya haura inda ya kai har mutum 92.

Wannan yana zuwa ne yayin da Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, yake shan caccaka sakamakon shillawa kasar waje da yayi hutu ba tare da ziyartar wadanda ibtila'in ya fadawa ba.

Kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Lawan Adam, ya tabbatar da cewa mutum 92 suka rasa rayukansu tsakanin watan Augusta zuwa Satumba sakamakon ambaliyar ruwan, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: An kai makura, dalibai sun toshe hanyar filin jirgin sama suna zanga-zanga

Gwamna Badaru
Ambaliyar Ruwa: Mutum 92 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Gwamna Ya Lula Yawon Shakawata Ketare. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Adam ya sanar da manema labarai a ranar Litinin cewa, da yawa daga cikin wadanda suka mutu ruwa ne ya tafi da su, ko tsawa ko kuma gini ya ruso musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium Times ta rahoto yadda dubban gidajen kasa, gadoji da tituna duk suka lalace sakamakon ambaliyar ruwan, lamarin da yasa jama'a suka dinga tururuwar komawa sansanin 'yan gudun hijira a jihar.

A yayin da ibtila'in ke cigaba da kamari, martanin gwamnatin jihar ya zama abun takaici.

A makon da ya gabata, wasu daga cikin wadanda suka koma sansanin 'yan gudun hijira a fadin jihar sun koka kan yadda gwamnati ta nuna halin ko in kula garesu.

Sun ce ba a samar musu da kayan rage radadi ba da na kiwon lafiya. Sun yi ikirarin cewa wasu daga cikin matan sun haihu a wurin ba tare da likitoci sun duba su ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Soludo ya Wanke Fulani, Ya Bayyana Wadanda ke Assasa Rashin Tsaro a Anambra

Amma a ranar 6 ga watan Satumba, Badaru ya sanar da tallafin N50 miliyan ga wadanda ibtila'in ya fadawa yayin da ya karba bakuncin 'dan takarar shugaban kasa a APC, wanda ya ziyarcesa domin ta'aziyya.

Wannan tallafin bai rage wata harzukar da wadanda lamarin ya ritsa da su ba, wadanda suka dinga hucin cewa gwamnatin jihar bata kara musu da komai ba.

Gwamna ya shilla kasar waje

Duk da wannan kiran da ake yi, gwamnan jihar ya shilla kasar waje hutu domin ya rage zafi kafin a fara gangamin yakin neman zabe.

Katsina: Yadda Rugugin Ruwan Kankara Ya Lalata Gonakin Jama'a

A wani labari na daban, wata gagarumar ruwan kankara ya lalata gonaki da gidajen jama'a a yankunan Dutsen-Kura/Kanya da Gozaki a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Malam Abdullahi Gozaki, wani mazaunin garin Gozaki ya sanar da Daily Trust cewa babu wani mutum daya da ya taba fuskantar irin wannan lamarin a yankin.

Kara karanta wannan

Fasto da mabiyansa sun sha bulala yayin da wasu tsageru suka farmaki coci a jihar Arewa

Yace gonakinsu, rufin gidaje da gilasan motoci duk suna lalace sakamakon ruwan kankarar da aka yi na tsawon mintuna.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel