An Tsige Shugaban Karamar Hukuma Guda a Jihar Filato Kan Wani Zargi

An Tsige Shugaban Karamar Hukuma Guda a Jihar Filato Kan Wani Zargi

  • Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban ƙaramar hukumar Langtang ta jihar Filato, Bitrus Zulfa Rimven, daga kan kujerarsa
  • Mambobin majalisar 14 daga cikin 18 ne suka kaɗa kuri'ar amince wa da kudirin sauke ciyaman ɗin kan wasu tihume-tuhume
  • Tun gabanin sauke shi a zaman yau Talata, Kansilolin sun sanar masa zargin da suke masa, amma ya gaza kare kansa

Plateau - An tunbuke shugaban ƙaramar hukumar Langtang ta arewa, Jihar Filato, Honorabul Bitrus Zulfa Rimven, daga kan kujerarsa.

Daily Trust ta rahoto cewa Honorabul Rimven ya rasa kujerarsa ne bayan mambobi 14 daga cikin 18 na majalisar Kansilolin ƙaramar hukumar sun amince ta kudirin tsige shi.

Wata majiya tace Kansilolin sun tsige shugaban ƙaramar hukumar ne ta hanyar kaɗa kuri'a a tsakininsu a zaman da suka gudanar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Jigon Jam'iyyar PDP Kuma Shugaban Wata Hukuma Ya Mutu Bayan Ya Yanke Jiki Ya Faɗi

Bitrus Zulfa Rimven.
An Tsige Shugaban Karamar Hukuma Guda a Jihar Filato Kan Wani Zargi Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Wakilin Leadership ya tattaro cewa tsigewar ta biyo bayan tuhumar da ake wa Ciyaman ɗin na sulalewar kuɗaɗe, wanda majalisar ta sanar masa tun mako biyu da suka shuɗe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zaman da suka yi karkashin jagorancin shugaban majalisar kuma Kansila mai wakiltar gundumar Pishe–Yashi, Hon. Maina Nanzing, ranar Talata, mambobin sun kaɗa kuri'ar tunɓuke Ciyaman ɗin.

Yadda Majalisar Kansilolin ta tsige Ciyaman

Jim kaɗan bayan fara zaman, Kansila mai wakiltar gundumar Jat, Hon. Dashe Yarnap, ya gabatar da kudirin tsige Ciyaman, Bitrus Rimven Zulfa, wanda ya samu goyon bayan mataimakin shugaba kuma kansila mai wakiltar gundumar Pajat.

Bayan gida ya amince da tunɓuke shugaban ƙaramar hukumar, Shugaban majalisa ya wuce wajen rantsar da mataimakiya, Nancy Philemon Paul, a matsayin Ciyaman.

Ƙe ake tuhumar Ciyaman ɗin har aka tsige shi?

Mataimakin shugaban majalisar Kansilolin, Hon. Dindam Longbap Wuyep, yace sun sanar da Ciyaman shirinsu na tsige shi a ranar 31 ga watan Agusta, 2022, idan har bai kare kansa ba.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin Da Yasa Muka Gaza Tunɓuke Shugaban PDP Kamar Yadda Wike Ya Bukata, Atiku

Daga cikin tuhume-tuhumen da ake wa tsohon Ciyaman ɗin har da kwashe kudi kimanin miliyan N300 daga aljihun gwamnati ta hanyar amfani da wani ma'aikacin ƙaramar hukuma, Samuel Malo.

Sauran zarge-zargen da ake masa sun haɗa da gaza naɗa majalisar zartarwa da zata tafiyar da harkokin gwamnati, inda ya cigaba da tafiyar da komai shi kaɗai kuma hakan ya saɓa wa dokoki.

A wani labarin kuma mun kawo muku cewa Jam'iyyar APC a Jihar Adamawa Ta Tsige Shugaba Daga Kujerarsa

Rikicin jam'iyyar APC a jihar Adamawa ya ƙara tsanani, kwamitin zartarwa ya tsige shugaban jam'iyya, Ibrahim Bilal.

Mai magana da yawun APC-Adamawa, Muhammed Abdullahi, yace sun ɗauki matakin ne kan zargin cin amana da karkatar da kuɗaɗe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel