Wajibi Ne Mu Lashe Zaben 2023 Don Kada Mu Kare a Kotu, Shugaban APC

Wajibi Ne Mu Lashe Zaben 2023 Don Kada Mu Kare a Kotu, Shugaban APC

  • Sanata Abdullahi Adamu yace sam ba zasu yarda su kare a kotu ba bayan zaben shugaban kasan 2023
  • Shugaban na APC ya bayyanawa matan da suka kai masa ziyara cewa ya zama wajibi jam'iyyarsa ta lashe zaben
  • Hukumar zabe ta INEC za ta gudanar da zaben shugaban kasan Najeriya ranar 28 ga Febrairu 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban uwar jam'iyar All Progressives Congress (APC), Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa jam'iyyarsa ba tada wani zabi da ya wuce ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Adamu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda ya karbi bakuncin uwargidar Bola Tinubu dan takaran shugaban kasan APC, Sanata Oluremi Tinubu, a ofishinsa dake Abuja, rahoton TheCable.

Remi Tinubu ta samu rakiyar Hajiya Nana, uwargidar Kashim Shettima, dan takaran kujeran mataimakin shugaban kasa, da sauran shugabannin mata na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Rade-radin Rigima: Bola Tinubu Ya Yi Bayani Kan Alakarsa da Shugaban APC na Kasa

Yace:

"Bari in yi amfani da wannan dama wajen fadin cewa bamu da wani zabi kuma ba zamu ji kunyan fadin haka ba."
"Ba zamu kare a kotu ba, amma Villa zamu kare. Masu kunne su ji."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Allah ya kare yan takaranmu kuma ya kara musu hikima. Mun yi alkawarin hada kai da dan takaran shugaban kasa da mataimakinsa."
"Saboda haka ina bada tabbacin tare zamu yi yakin nan. Duk abinda kuke bukata zamu baku don mu samu nasara."
Adamu
Wajibi Ne Mu Lashe Zaben 2023 Don Kada Mu Kare a Kotu, Shugaban APC Hoto: APC
Asali: UGC

Bola Tinubu Ya Yi Bayani Kan Alakarsa da Shugaban APC na Kasa

Asiwaju Bola Tinubu mai harin zama shugaban Najeriya a karkashin APC yace babu rikici tsakaninsa da shugaban jam’iyyarsa, Abdullahi Adamu.

Vanguard tace Asiwaju Bola Tinubu ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba 2022, a nan ya gana da shugabanninsa.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban CAN ya magantu kan abin da ya kamata fastoci su yi a lamarin jam'iyya

Bola Tinubu ya musanya rade-radin da ake yi na cewa babu jituwa tsakaninsa da Sanata Abdullahi Adamu wanda yake rike da shugaban APC a matakin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel