Hotuna da Bidiyon shagalin Gaɗa da aka yi na bikin Gimbiya Ruƙayya Bayero

Hotuna da Bidiyon shagalin Gaɗa da aka yi na bikin Gimbiya Ruƙayya Bayero

  • Kyawawan hotuna da bidiyoyi daga wurin shagalin gada ko ranar kauyawa ta auren Fulani Rukayya Bayero sun kayatar
  • Amaryar ta fito shar cikin shigar gargajiya inda ta daura kallabi sannan ta saka mayafi mai matukar daukar hankali
  • Gidan sarautar Kano ya cika makil da kawayen amaryar, 'yan uwa da abokan arziki wadanda suka je taya ta murnar babbar ranarta dake zuwa

Kano - Bidiyoyi da hotunan shagalin gada ko kuma ranar kauyawa ta auren Fulani Rukayya Bayero sun matukar daukar hankulan jama'a.

Wannan shagalin shine na uku a jerin shagulgulan bikin auren kyakyawar diyar sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero.

Fulani Rukayya Bayero
Hotuna da Bidiyon shagalin Gaɗa da aka yi na bikin Gimbiya Ruƙayya Bayero. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

An fara ne da shagalin kamu tun a ranar Lahadi, a ranar Litinin aka biye shi da shagalin Lugude wanda a gargajiyance aka yi shi inda masu kidan kwarya da shantu suka baje kolinsu.

Kara karanta wannan

Al’ada Mai Ban Sha’awa: Bidiyoyin Shagalin ‘Lugude’ Na Bikin Ruqayya Bayero, Amarya Da Kawayenta Sun Sha Daka

Sai a ranar Talata ne aka yi shagalin kauyawa ko kuma gada wanda amaryar tayi shigar gargajiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shigar da kyakyawar amaryar tayi ya matukar daukar hankali inda ta fito cikin shigarta ta alfarma cike da izza.

Ga hotunan da biyoyin wurin ku sha kallo:

Ba amaryar kadai ta bada kala a wurin wannan gadar ba, Sarauniya Hadiza Bayero, mahaifiyar amarya ma tayi fes da ita inda ta haska a wurin taron, kamar yadda shafin @fashionseriesng suka wallafa a Instagram.

Kyawawan Hotuna da Bidiyo Daga Kamun Kabiru Aminu Bayero da Tsuleliyar Amaryarsa

A wani labari na daban, kyawawan hotuna da bidiyoyin wurin kamun ango Kabiru Aminu Bayero da zukekiyar amaryarsa, Aisha Ummarun Kwabo sun matukar kayatar da jama'a.

Biki tuni dai ya kankama inda ake hango ranar daurin aure, Juma'a, 26 ga watan Augustan 2020 a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Daba Sun Kone Gidan 'Yan Shi'a, Kadarorin N3m Sun yi Kurmus

A daren Laraba ne aka fara da shagalin bikin auren inda kamun da aka yi ya matukar kayatarwa ganin yadda kyakyawar amaryar ta fito shar cikin shiga ta alfarma da kwalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel