Matakan Da Dan Najeriya Zai Bi Don Karban Dukiyar Dan'Uwansa Da Ya Mutu A Ingila

Matakan Da Dan Najeriya Zai Bi Don Karban Dukiyar Dan'Uwansa Da Ya Mutu A Ingila

 • Gwamnatin kasar Birtaniya na neman iyalan yan Najeriya 56 da suka mutu a kasar suka bar dukiya
 • Ga duk wanda ke da dan'uwa kuma yana son zuwa karan dukiyar da suka bari, sai da bada hujjoji
 • Gwamnatin Birtaniya ta gindaya matakai 15 da mutum zai dauka don tabbatar da gaskiyar maganar

Kalamai da dama sun biyo bayan labarin cewa gwamnatin Birtaniya na neman iyalan wasu yan Najeriya da suka mutu a kasar suka bar makudan dukiya babu magada.

Gwamnatin tace duk wande sunan dan'uwansa ke cikin wannan suna ya garzayo, a sanarwar da tayi a shafinta na yanar gizo.

Amma ba haka kawai za'a ba mutum ba, akwai matakan da zai dauka.

Gidaje
Hanyoyi 15 Da Dan Najeriya Zai Iya Karban Dukiyar Dan'Uwansa Da Ya Mutu A Ingila

Legit.ng a baya ta kawo muku jerin sunayen wadanda suka mutu masu dukiya ba'a ga 'yan uwansu ba.

Kara karanta wannan

Na Ga Al'arshin Ubangiji: In Ji Bokan Da Ya Farka Daga Akwatin Gawa Kwana Biyu Bayan Mutuwarsa A Nasarawa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jerin wadanda ke da hakkin gan gadon

A cewar gwamnatin UK, wadannan sune jerin masu hakki kan gadon:

 • Miji ko Mata
 • 'Da, jika, tattaba-kunne
 • Mahaifi ko Mahaifiya
 • Kani, kanwa masu uwa 'daya uba 'daya ko 'yayansu
 • Uba 'daya amma ba 'uwa daya ba ko Uwa daya ba Uba daya ba
 • Kakanni
 • Kannen Uba Ko na Uwa
 • Kannen Uba ko Uwa ta bangaren Kakanni (Namiji ko Mace)

Matakan karban dukiyar

A cewar gwamnatin Birtaniya, duk wanda ya ke da 'danuwa ya tuntubi Bona Vacantia division (BVD) mai hakkin ajiye bayanan wadanda suka mutu ba suyi wasiyya ba.

A cewar gwamnatin:

"Idan ka san ka cancanci gadon wannan dukiya wanda BVD ke kula da su, ka kawo hujjar dangi cewa kai jinin wanda ya mutu ne."
"Idan aka ga akwai alamun gaskiya ka cancanta, BVD zai bukaci ka gabatar da wasu takardun hujjar nuna cewa ka cancanta."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Kame Tukur Mamu ba zai hana mu ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja ba

Takardun da za'a bukata

 • Takardar shaidar ranar haihuwa (dauke da sunan iyaye) da takardar shaidar auren na dukkan wanda ke tsakaninka da mamacin
 • Takardun shaidan cewa nuna sunanka da adireshinka na gaske ne
 • Cikakken bayani, tare da hujjoji, kan wani takarda da ya bace (amma ka sani wannan iya zama matsala)

Akwatin sakon email da za'a iya tura sako shine bvestates@governmentlegal.gov.uk

Wasu bayanan na nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel