Idan Siyasa Ƙazamin Harka Ne, Kiristoci Su Shiga Daga Ciki Su Tsaftace Shi, In Ji Babban Limamin Coci

Idan Siyasa Ƙazamin Harka Ne, Kiristoci Su Shiga Daga Ciki Su Tsaftace Shi, In Ji Babban Limamin Coci

  • Zababen babban limamin cocin Methodist Na Nigeria, Archibishop Oliver Abah ya karfafawa kiristoci gwiwa su shiga siyasa
  • Malamin addinin ya ce galibin kiristoci suna kyamar siyasa saboda kalon da ake yi masa a matsayin kazamin harka amma hakan shine dalilin da yasa dole masu tsoron Allah su shiga su tsaftace shi
  • Archibishop Abah ya yi wannan jawabin ne a lokacin da dan takarar kujerar sanata na Benue South karkashin APC, Kwamared Daniel Onjeh ya kai masa ziyara a gidansa

Benue - Dan takarar kujerar sanata na jam'iyyar APC a Benue South, Kwamred Daniel Onjeh, a jiya ya ziyarci zababen Archbishop na cocin Methodist, Archibishop Oliver Abah, a gidansa da ke Otukpo, jihar Benue.

Archbishop Abah ya tarbi Onjeh da tawagarsa tare da wasu manyan limaman cocin na Methodist kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Idan Na Taba Satar Kudin Gwamnati, Allah Ya Tsine Mana Albarka, Peter Obi

Kwamred Onjeh da Archbishop
'Idan Siyasa Kazamin Harka Ne, Kiristoci Su Shiga Daga Ciki Su Tsaftaace Shi', In Ji Archibishop Abah. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke magana a wurin taron, Onjeh ya ce ya yi murnar jin labarin nadin Archbishop Abah a matsayin zababen Prelate na Cocin Methodist na Najeriya.

Onjeh ya ce nadin na Archbishop Abah - kasancewarsa dan Arewa na farko da ya kai matsayin - ya faranta masa rai sosai kuma yana alfahari da shi.

Ya kuma ce mutane Benue na Kudu da sauran yan jihar duk suna taya shi murna da alfahari da shi.

Martanin Archibishop Oliver Abah

A bangarensa, Archibishop Abah ya gode wa Onjeh da tawagarsa bisa ziyarar da suka kawo masa ya yi addu'ar Allah ya tsaita ransu.

Limamin cocin ya ce duk da cewa baya siyasan jam'iyya, yana bibiyar siyasar Onjeh; kuma yana masa fatan alheri.

A shiga daga ciki a yi gyara - Archibishop Abah

Kara karanta wannan

Ba zai yiwu a bar Shettima ya kula da tsaron Najeriya ba, jigon PDP ya fadi dalili

Archibishop Abah ya kara da cewa akwai wata al'ada tsakanin kiristoci na cewa siyasa harka ce mai kazanta, don haka mafi yawancinsu suke guje wa siyasa.

Amma, malamin addinin ya ce idan siyasa kazamar harka ce, wannan ma babban dalili ne da ya kamata kiristoci su shiga daga ciki domin su kawo gyara.

Ya kara da cewa Onjeh dan siyasa ne mai nagarta kuma zai samarwa mutane romoon demokradiyya idan ya ci zabe, domin hakan shine kawai hanyar da mutane za su san ana gwamnati.

Gwamnan Arewa Ya Shawarci Kirista Su Shiga Siyasa Don Dawo Da Martabar Najeriya

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom ya bukaci kiristoci su shiga siyasa wanda ya ce zai taimaka a dawo da martabar Najeriya, rahoton Nigerian Tribune. Da ya ke magana yayin gana wa da mambobin Knight of St.

Mulumber, Abuja karkashin jagorancin Sir Michael Awuhe a ranar Juma'a, gwaman ya ce kuskure ne kiristoci su rika yi wa siyasa kallon kazamar wasa.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel