Bai Kamata a Bar Lamarin Tsaro Ga Kashim Shettima Ba, Inji Jigon Jam’iyyar PDP

Bai Kamata a Bar Lamarin Tsaro Ga Kashim Shettima Ba, Inji Jigon Jam’iyyar PDP

  • Jiga a jam'iyyar adawa ta PDP, Anthony Ehilebo ya shawarci 'yan Najeriya da kada su yarda da batun APC da 'yan takarar ta
  • Kashim Shettima ya yi alkawarin kulawa da lamurran tsaro a Najeriya bayan sun lashe zaben shugaban kasa a 2023
  • Kashim Shettima dai tsohon gwamna ne a jihar Borno, kuma Tinubu ya zabe shi a matsayin abokin takara a zaben 2023

Najeriya - Jigon jam'iyyar PDP ya hango matsala, ya gargadi 'yan Najeriya da su kula da gamin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, rahoton Punch.

Anthony Ehilebo, ya shawarci 'yan Najeriya da cewa, kada su bari Kashim Shettima ya kusanci kujera a Villa, don kada ya kula da lamurran tsaro a Najeriya.

Jigon na PDP ya bayyana hakan ne yayin wata tattauna na shirin Politics Today na Channels Tv a ranar Lahadi, 28 ga watan Agustan bana.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

Jigon PDP ya gargadi 'yan Najeriya, ya ce kada su bari batun tsaro ya koma hannun Shettima
Bai Kamata a Bar Lamarin Tsaro Ga Kashim Shettima Ba, Inji Jigon Jam’iyyar PDP | Hoto: Adoyi Ali
Asali: Facebook

A wani taro da aka yi a jihar Legas na kungiyar lauyoyi ta Najeriya, Shettima ya ce zai dabbaka abin da ya aikata jihar Borno na mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, ya ce Tinubu ya zai kawo ci gaba Najeriya kamar yadda ya daidaita zaman jihar Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya, Daily Post ta ruwaito.

Martanin Ehilebo

Da yake martani ga batun Shettima a ranar taron na lauyoyi, jigon PDP Ehilebo ya ce:

"Ta yaya za ka zo taron NBA ka bayyana kai tsaye a talabijin cewa za ka magance tsaro kuma abokin takarar kuma zai kula da fannin tattalin arziki?
“Sashe na 130(2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya fada kara cewa aikin Babban Kwamandan Sojoji ne.
"Kuma idan ma zai saryar da ikon hakan, to sai dai ga sojojin kasar. Amma gashi anan mun samu dan takarar mataimakin shugaban kasa da ke fada wa duniya cewa zai kula da tsaron kasa."

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki

Martani daga jigon APC

Shi kuwa da yake kare Shettima, masanin tattalin arziki kuma jigon tafiyar gangamin Tinubu da Shettima, Ayo Oyalowo, ya ce kwata-kwata mutane basu fahimci abin da Kashim Shettima ke cewa bane.

Irin Mulkin da Muka Yi a Borno da Legas, Shi Za Mu Yiwa Najeriya, Inji Abokin Takarar Tinubu

A wani labarin, abokin takarar Tinubu a zaben 2023, Kashim Shettima ya bayyana irin tagomashin da suka shiryawa 'yan Najeriya, Channels Tv ta ruwaito.

Shettima ya ce, abubuwan mamaki da Bola Tinubu ya yi jihar Legas sadda yake gwamna su ne za su kasance a Najeriya bayan 2023.

Hakazalika, ya ce za su surka da irin ababen da ya yiwa jihar Borno, domin ganin an samu ci gaba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel