2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

  • Sakataren kungiyar mayu da matsafa na Najeriya (WITCAN), Dakta Okhue Iboi ya goyi bayan tikitin musulmi da musulmi na APC
  • Dakta Iboi ya ce zaben Kashim a matsayin abokin takara da Bola Tinubu ya yi ba zai kawo wata matsala a shugabancin kasar ba
  • Ya kuma jadada cewa kungiyar za ta sanar da wanda zai zama shugaban Najeriya gabanin zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Cif Okhue, kakakin kungiyar Fararen Mayu da Matsafa ta Najeriya (WITZAM), ya ce babu wani matsala don jam'iyyar APC ta tsayar da musulmi biyu a takarar shugaban kasa da mataimaki.

Ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke bayyana cewa nan bada dadewa ba kungiyar za ta hango wanda zai zama shugaban kasa a 2023, Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Dan Siyasan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bayyana Dan Takarar Da Zai Gaji Kuri'u Miliyan 12 Na Buhari A Arewa

Shettima da Tinubu
2023: Kungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Karfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC. Hoto: @OfficialBAT.
Asali: Twitter

Da ya ke magana da manema labarai a Legas, Iboi ya ce yan takara masu addini daya bai taba zama matsala a Najeriya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cif Okhue Oboi ya kara fadada bayani

Ya bada misali da Abiola-Kingibe da suka ci zaben shugaban kasa na 2023, fitaccen mai maganin gargajiyan, amma, ya ce dan takarar na APC, Bola Tinubu, da abokin takararsa, Kashim Shettima, za su fuskanci kallubale daga wasu jam'iyyu.

Da aka masa tambaya ko Tinubu zai ci zabe, Iboi ya ce:

"Tinubu ba mutum bane kamar kowa. Mutum ne mai hangen nesa. Idan ya kwanta barci, za a fada masa abin da zai yi da hanyoyin da zai bi don aikata abin. Ba zanyi mamaki ba idan an fada masa abin da zai yi, kafin ya zabi abin takararsa."

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Zabi Dan Siyasan Arewa Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa

A wani rahoton, Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC, ya fadawa takwararsa na LP, Mista Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da ma sauran yan takara.

Tinubu, cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Mista Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya gargadi magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel