Gwamnan Arewa Ya Shawarci Kirista Su Shiga Siyasa Don Dawo Da Martabar Najeriya

Gwamnan Arewa Ya Shawarci Kirista Su Shiga Siyasa Don Dawo Da Martabar Najeriya

  • Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ya shawarci kiristocin Najeriya su rika shiga siyasa ana dama wa da su don dawo da martabar Najeriya
  • Ortom ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga ta mambobin cocin Knight of St. Mulumber reshen Abuja karkashin jagorancin St. Michael Awuhe
  • Ortom ya ce kuskure ne kirista su rika zama a gefe guda suna cewa siyasa kazamin wasa ne, yana mai cewa su tafi su yi rajistan zabe su kuma shiga a fafata da su don yaki ake a kasar

Jihar Benue - Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom ya bukaci kiristoci su shiga siyasa wanda ya ce zai taimaka a dawo da martabar Najeriya, rahoton Nigerian Tribune.

Da ya ke magana yayin gana wa da mambobin Knight of St. Mulumber, Abuja karkashin jagorancin Sir Michael Awuhe a ranar Juma'a, gwaman ya ce kuskure ne kiristoci su rika yi wa siyasa kallon kazamar wasa.

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

Gwamnan Arewa Ya Shawarci Kirista Su Shiga Siyasa Don Dawo Da Martabar Najeriya
Gwamnan Benue Ya Shawarci Kirista Su Shiga Siyasa Don Dawo Da Martabar Najeriya. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi kira ga shugabannin kiristoci su karfafa wa mambobinsu gwiwa su yi rajistan katin zabe da aka yi a yanzu.

Newstral ta rahoto cewa Ortom ya ce idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a kasar, yanzu tamkar yaki ake yi.

Yaki ake yi a Najeriya a halin yanzu, Gwamna Ortom

Ya ce:

"Ana yaki ne a Najeriya a yanzu da muke magana. Kiristocin da ke gefe suna cewa siyasa kazamin wasu ne kuskure suka yi. Su fito su nemi mukamai su nuna sha'awar mayar da kasa kan turba mai kyau.
"Yanzu lokacin tantance kadin zabe ne, mu hada kan mutanen mu su yi rajista su kuma kada kuri'a, ya kara da cewa, kirista su hada kai a matsayinsu na coci domin yan ta'adda sun mamaye kasar nan."

Kara karanta wannan

Tsadar fom din takara: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, inji wani dan takaran APC

Ortom ya mika godiyarsa ga cocin katolika saboda jajircewa wurin aikin Ubangiji yana mai cewa suna cikin coci mafi tsari a Najeriya.

Ya kuma goda wa cocin bisa shawarwari da goyon bayan da ta ke bashi.

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel