Zamu Karbi Sabon Bashin N11tr Kuma Zamu Sayar Da Wasu Dukiyoyin Gwamnati A Shekarar 2023, Minista Zainab

Zamu Karbi Sabon Bashin N11tr Kuma Zamu Sayar Da Wasu Dukiyoyin Gwamnati A Shekarar 2023, Minista Zainab

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana hanyoyi biyu da zata iya samun kudin albashi da ayyuka a 2023
  • Ministar Kudi ta bayyana cewa gwamnati za ta iya biyan kudin tallafin mai zuwa bayan zabe
  • Najeriya ta karbo basussuka da dama daga wajen kasar Sin, Bankin Duniya da Asusun lamunin duniya

Abuja - Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata karbi sabon bashin sama da N11 trillion tare da sayar da dukiyoyin gwamnati don kasafin kudin 2023.

Ta bayyana cewa gwamnati zata bukaci kudi N12.42 Trillion idan har zata cigaba da biyar tallafin mai a 2023.

Hajiya Zainab ta bayyana hakan ne ranar Litnin yayinda ta bayyana gaban yan majalsar wakilai, rahoton PremiumTimes.

Zainab
Zamu Karbi Sabon Bashin N11tr Kuma Zamu Sayar Da Wasu Dukiyoyin Gwamnati A Shekarar 2023, Minista Zainab
Asali: UGC

Ta yi bayanin cewa zabi biyu gwamnati ke da shi, na farko a cigaba da biyan kudin tallafin mai a 2023 gaba daya ko kuma a biya na watanni shida kadai (zuwa bayan zabe).

Kara karanta wannan

Buhari ya fadi kudaden da ya kashe wajen gyara ofisoshin 'yan sanda da bariki a cikin shekaru 3

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarta, idan aka biya kudin har karshen shekara, ana bukatar N12.41 Trillion a 2023. Amma idan zuwa watan Yuni bayan zabe za'a biya, N6.72 trillion za'a kashe kan tallafin mai.

Ta kara da cewa da kamar wuya a iya biyan kudin tallafin gaba daya dubi da halin da ake ciki yanzu, amma idan aka biya na watann shida kadai da 'dan sauki.

A cewarta, idan aka biya na wata shida, za'a iya karban bashin N9.32 trillion don cikasa kasafin kudin 2023.

Wannan zai hada da N7.4trn daga bankunan gida, sannan N1.8trn daga kasashen waje.

'Yan Majalisa Sun Gayyaci Ministar Kudi, Suna Neman Takardun Tallafin Man Fetur

Mun kawo muku cewa Majalisar wakilai ta gayyaci ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Hajiya Zainab Ahmed domin ta gabatar da dukkan takardun da suka shafi batun tallafin mai daga 2013 zuwa yau.

Kara karanta wannan

An Tsaida Ranar da Kwankwaso Zai Yi Jawabi a Chatham House, Zai Tallata Manufofinsa

Ibrahim Aliyu, shugaban kwamitin wucin gadi na musamman da ke binciken tsarin tallafin man fetur ne ya bayyana hakan a lokacin da Stephen Okon, Daraktan kudi na cikin gida a ma’aikatar ya bayyana a gabansa a Abuja ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel