Da duminsa: EFCC Tayi Ram da Daraktan Asusu na NDDC Kan Damfarar N25b

Da duminsa: EFCC Tayi Ram da Daraktan Asusu na NDDC Kan Damfarar N25b

  • Hukumar EFCC ta cafke daraktan kudi da asusu na hukumar cigaban yankin Niger Delta, Eno Ubi Otu kan zarginsa da damfara
  • Ana zargin Otu ne da hannu kan waskar da makuden kudade har N25 biliyan na harajin hukumar da aka kasa gano inda suka yi
  • Kamar yadda majiya daga EFCC ta tabbatar, an cafke shi tun karfe 11:15 na safe kuma yana amsa tambayoyi har karfe 7:15 na dare ba a sake shi ba

FCT, Abuja - Daraktan kudi da asusu na Hukumar Cigaban Niger Delta, NDDC, Eno Ubi Otu, a halin yanzu yana hannun jami'an Hukumar Yaki da Rashawa tare da Hana Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC.

Daily Trust ta ruwaito, an gano cewa, jami'an hukumar EFCC sun cafke Otu wurin karfe 11:15 na safe sakamakon zarginsa da ake yi da alaka da waskar da sama da N25 biliyan ta haraji.

Kara karanta wannan

Diraktan Hukumar FCCPC Ya Mutu Bayan Fada Da Abokiyar Aiki a Katsina

Akanta Janar na NDDC
Da duminsa: EFCC Tayi Ram da Akanta Janar na NDDC Kan Damfarar N25b
Asali: UGC

Wata majiya daga hukumar da ta sirranta da Daily Trust, tace jami'in NDDC din yana hannun jami'an hukumar har zuwa 7:15 na yammacin yau Laraba.

Kamar yadda jami'in yace, kamne Otu yana daga cikin binciken da ake yi kan rahoton kashe kudin hukumar NDDC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk kokarin jin ta bakin kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren da aka yi, ya gagara don baya daukar wayarsa.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel