Ni Na Kashe Sheik Goni Aisami, Jami'in Soja Da Aka Kama Ya Laburtawa Yan Sanda

Ni Na Kashe Sheik Goni Aisami, Jami'in Soja Da Aka Kama Ya Laburtawa Yan Sanda

  • Hukumar yan sanda ta bayyana sakamakon bincikenta kan Sojojin da akewa zargin kisan Sheih Goni Aisami
  • Bayan amsa laifinsu, hukumar ta ce ana kammala binciken gaba daya za'a gurfanar da su gaban kuliya
  • An yi jana'izar Shehin Malamin mazauni jihar Yobe ranar Asabar kuma dubban mutane sun hallara

Yobe - Hukumar Yan sandan a Jihar Yobe, a ranar Talata, ta yi bayanin yadda wani Soja, Kofur John Gabriel, ya halaka Shehin Malami, Goni Aisami, a karamar hukumar Karasuwa ta jihar.

Kakakin hukumar, Dungus AbdulKarin, a jawabin da ya fitar yace an damke Gabriel ne tare da abokin aikinsa, Adamu Gideon, dake aiki a 241 Recce Battalion, Nguru, rahoton PremiumTimes.

A cewarsa:

"Yayin gudanar da bincike, Sojojin sun amince lallai sun aikata laifin. Har yanzu dai ana bincike kuma suna hannun yan sanda."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Kauran Katsina Kuma Hakimin Rimi, Nuhu Abdulkadir, Rasuwa

"Ana kammala bincike za'a gurfanar da su gaban kotu."
Gideon Gabriel
Ni Na Kashe Sheik Goni Aisami, Jami'in Soja Da Aka Kama Ya Laburtawa Yan Sanda Hoto: John G/Adamu Gideon
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda Suka Kashehi

DSP Dungus Abdulkarim, yayi bayanin ainihin abinda ya faru tsakanin marigayin da Sojojin.

A jawabinsa:

"Sheikh Gani Aisami, wani shahrarren Malamin addinin Islama a Gashua yana tafiya shi kadai daga Kano zuwa Gashua a motarsa Honda Acord mai Lamba KBT 31 AE sai yaci karo da Sojoji a Nguru."
"Sai Gabriel ya bukaci Malamin ya rage masa hanya zuwa Jaji Maji kuma Malamin ya amince. Kafin su kai Jaji-Maji, sai Gabriel ya fadawa Malamin ya tsaya wani abu na 'kara a tayar baya."
"Lokacin da Malamin ya sauka duba tayar kawai sai Sojan ya fito da bindigarsa ya harbeshi har lahira."
"Ya shigar da gawarsa cikin daji ya boye kuma ya dauki motar amma taki tashi."

Kakakin yan sanda ya cigaba da cewa sai Soja ya kira abokin aikinsa Gideon tare da Bakanike don a gyara motar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sheke Babban Sojan Najeriya a jihar Anambra

"Amma asirinsu ya tonu lokacin da wani manomi ke hanyar tafiya gonarsa sai ya ga gawar da mota kuma suka sanar da yan sanda a Jaji," DSP AbdulKarim yace

"Haka aka damke Sojojin biyu kuma aka dauki gawar Malamin, motarsa da bindigar da akayi amfani wajen aikata laifin."

Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa

Kwana guda bayan Jana'izarsa, hotunan motar Sheikh Goni Aisami, da ake zargin wasu Sojoji da kashewa a hanyar Gashua zuwa Kano sun bayyana.

Rahotanni sun gabata cewa jami'an Sojojin sun kashe babban Malamin ne saboda kwace motarsa kirar Honda Accord (2006).

Kalli hotunan motar kamar yadda sashen Hausa na BBC ta wallafa

Asali: Legit.ng

Online view pixel