Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa

Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa

  • An gano motar da ake zargin wasu Sojoji da sacewa na Sheih Goni Aisami bayan ya taimaka ya rage musu hanya
  • Hukumar Soji ta saki jawabinta ta farko kan wannan lamari inda tace zata gudanar da bincike kai
  • An yi jana'izar Shehin Malamin mazauni jihar Yobe ranar Asabar kuma dubban mutane sun hallara

Jihar Yobe, Najeriya - Kwana guda bayan Jana'izarsa, hotunan motar Sheikh Goni Aisami, da ake zargin wasu Sojoji da kashewa a hanyar Gashua zuwa Kano sun bayyana.

Rahotanni sun gabata cewa jami'an Sojojin sun kashe babban Malamin ne saboda kwace motarsa kirar Honda Accord (2006).

Kalli hotunan motar kamar yadda sashen Hausa na BBC ta wallafa:

Motar
Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa @bbchausa
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wani Da Ya Karanci Injiniyanci Ya Sace Injin Mota Na N2m Daga Jami'a, Ya Sayar N30,000 A Kasuwa

Motar
Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa
Asali: Twitter

Motar
Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa
Asali: Twitter

Aisami
Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa
Asali: Twitter

Yadda Sheikh Aisami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi

Bayanai sun gabata kan mutuwar Sheikh Goni Aisami, fitaccen malamin addinin Islama na Yobe jihar Yobe wanda aka bindige a ranar Juma'a.

Kamar yadda DSP Dungus Abdulkarim, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe ya bayyana, mutum biyun da ake zargi sojoji ne daga bataliya ta 241 sake Recce a Nguru sun shiga hannu.

Daily Trust ta rahoto cewa, yace lamarin ya faru wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan Aisami ya ragewa daya daga cikin wadanda ake zargin hanya.

Kakakin rundunar 'yan sandan yace Aisami na tuka motar daga Gashua zuwa Nguru, lokacin da wanda aka zargin ya tsayar da shi da kayan gida dauke da gado kuma ya roki malamin da ya rage masa hanya zuwa Jaji-Maji.

"A lokacin da suka kusa Jaji-Maji, malamin ya tsayar da motar domin biyan bukata," yace inda yana dawowa wanda ake zargin ya fito da Ak-47 ya bindige shi har sau biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah Ya Yiwa Kauran Katsina Kuma Hakimin Rimi, Nuhu Abdulkadir, Rasuwa

Abdulkarim ya kara da cewa, wanda ake zargin ya yi kokarin tserewa da motar mamacin amma ya kasa saboda makalewa da tayi a tabo kuma ta kasa fitowa.

"Ya daga waya ya kira dayan wanda ake zargin wanda ya isa wurin da wata motar, sai dai ta lalace a take.
"Wadanda ake zargin sun nemi taimako daga wata kungiyar 'yan sa kai dake Jaji-Maji. Lokacin da kungiyar ta iso wurin, sai aka samu gawar Aisami," Kakakin 'yan sandan yace.

Abdulkarim ya kara da cewa, kungiyar 'yan sa kan ta gaggauta kiran 'yan sanda inda aka cafke wadanda ake zargin.

Ya bayyana cewa, 'yan sandan sun samo bindiga da motocin biyu inda ya kara da cewa ana kokarin gano su waye wadanda ake zargin.

Abdulkarim yace za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan kammala bincike a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel