Yar-Shekara-12 Kuma 'Yar JSS1 Ta Samu Admishon Shiga Jami'a Saboda Kwakwalwarta

Yar-Shekara-12 Kuma 'Yar JSS1 Ta Samu Admishon Shiga Jami'a Saboda Kwakwalwarta

  • Jessica Okonye, 'Yar-shekara-12 ta samu gurbin karatu a jami'ar Admiralty University of Nigeria matsayin daliba mai lura
  • Jessica wacce 'yar aji daya ce a makarantar sakandare ta nuna bajinta da kwarewa gaban wasu manyan Farfesoshi
  • Farfesa John Alizor, wani tsohon Malami a jami'ar Amurka ne ya gano wannan yarinya mai baiwa

Wata yar ajin JSS1 a makarantar sakandare, Jessica Okonye, ta samu gurbin karatu a jami'ar Sojojin ruwan Najeriya watau Admiralty University of Nigeria, Ibusa, dake jihar Delta.

Jessica ta samu wannan gurbin karatun ne bayan Farfesa John Alizor ya gano yarinya ce mai baiwa kuma mai kokarin gaske.

An ruwaito cewa Jessica ta ci karo da Farfesan ne a wani shago inda take koyon aiki. Kawai sai ya fara bata horo.

Kara karanta wannan

Atiku: Sai na mai da jami'o'in tarayya karkashin gwamnatin jiha idan na gaji Buhari a 2023

Daga baya Farfesan ya fara bata ayyuka tana yi har ya gamsu da ita.

Jessica
Yar-Shekara-12 Kuma 'Yar JSS1 Ta Samu Admishon Shiga Jami'a Saboda Kwakwalwarta
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gabanin bata wannan gurbi na karatu, ta tattauna da shugabannin jami'ar inda suka tabbatar da lallai tana da baiwa kuma suka gamsu da ita.

Me ake nufi da 'Daliba mai lura'

Jami'ar a jawabin da ta fitar a shafin Facebook, tace Shugaban jami'ar, Farfesa Paul Omojo Omaji yace:

"Shugaban jami'a ya tabbatar lallai Jessica na da kokari. Ya kara da cewa bayan gudanar da wani bincike dake nuna zata ita jure karatun jami'a ba tare da kammala sakandare ba, jami'ar ADUN zata dauke matsayin daliba mai lura."
"Ya kara da cewa Dalibai mai lura itace wacce za ta rika shiga aji karatu ba tare da niyyar samun kwali ba."

Idan Jessica ta samu shiga jami'ar, za ta zama daliba mafi karancin shekaru da ta samu shiga jami''a a Najeriya.

Kara karanta wannan

Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa

Alena Wicker: Yarinyar Mai Shekaru 13 Da Ta Samu Shiga Jami'a Don Karatun Likita

A wani labarin mai kama da wannan, a ranar 30 ga watan Yuni, Alena Wicker, yarinyar mai shekaru 13 ta sanar cewa ta samu gurbin karatu a Jami'ar Alabama da ke Birmingham Heersink domon karatun likitanci.

Hakan na nufin ita ce mutum mafi karancin shekaru wacce ta samu shiga jami'ar ta Alabama don yin karatun likitanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel