Kungiyar CAN Za Ta Fallasa Makarantun da ake Muzgunawa Kiristoci a Najeriya

Kungiyar CAN Za Ta Fallasa Makarantun da ake Muzgunawa Kiristoci a Najeriya

  • Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta bukaci a fara tattaro sunayen da ake cin zarafin Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya ta bada umarni a ba kowace makaranta damar gina coci a fadin Najeriya
  • CAN tana zargin har yanzu akwai makarantun da kiristoci ba su samun damar yin bauta da kyau

Kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN ta umarci shugabanninta na jihohi da shiyyoyi da su gabatar da sunayen makarantun da ake muzguna masu.

Jaridar Punch tace kungiyar ta CAN ta na zargin akai wasu makarantun kasar nan da suka maida kiristoci saniyar ware, suke nuna masu bambanci.

Nan gaba kadan CAN za ta saki sunayen wadannan makarantun gaba da sakandare da aka hana kiristoci su gina cocinsu domin su bautawa Ubangiji.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

A lokacin da aka ba musulmai damar gina wuraren ibada a makarantun, kungiyar ta CAN na zargin cewa ba a ba kirostoci damar gina majami'ansu ba.

Rahoton da muka samu ya nuna Sakatare Janar na CAN, Joseph Daramola, ya bada wannan umarni ga jami'an da ke jagorantar aikin kungiyar a kasa.

Umarnin da Adamu Adamu ya bada

Daramola yake cewa duk da Ministan ilmi, Adamu Adamu ya bada umarni ga duk makarantu su kyale kiristoci su gina cocinsu, hakan bai tabbata ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban CAN
Sabon Shugaban CAN Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Adamu Adamu yana so kiristoci su rika yin ibadarsu ba tare da tsangwama ko bata lokaci ba, shugabannin wasu makarantu sun ki daukar umanin.

“Daga yanzu zuwa 19 ga watan Agusta, an umarce ni da rubutawa duka shugabannin shiyyoyi da na jihohi na kungiyar nan, da su kawo sunayen makarantun da aka hana a gina coci, inda za a rika haduwa domin yin ibada a ranakun Asabar da Lahadi.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Masu Safarar Kwayoyi da Yan Bindiga Sama da 100 a Jihar Arewa

CAN za ta dauki matsaya

Jawabin Joseph Daramola yake cewa ba da dadewa ba CAN za ta dauki matsaya a kan wannan tsari na maida wasu mabiya addinin kirista saniyar ware.

Takardar ta jinjinawa shugabannin addinin na Kirista, tare da nuna sa ran za a ji daga karensu.

A karshe kungiya ta tabbatar da cewa za ta cigaba da kokari da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da cewa mabiya kowane addini sun samu ‘yanci.

Badakala a PSC

A wani rahoto, an gano cewa an batar da N447m da sunan aikin kafinta, kuma N200m sun tafi wajen wasu kwangiloli da ba a san kan su ba a PSC,

A wasikar da Naja’atu Muhammad ta aikawa Hukumar EFCC, za a ji zargin yadda Shugaban PSC, Musiliu Smith yake facaka da dukiyar gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel