Hotuna da Bidiyoyi: Shigar alfarmar da Surayya Sule Lamido Tayi a Liyafar Jajiberin Aurenta ya Kayatar

Hotuna da Bidiyoyi: Shigar alfarmar da Surayya Sule Lamido Tayi a Liyafar Jajiberin Aurenta ya Kayatar

  • Kasaitacciyar shigar alfarmar da Surayya Sule Lamido tayi wurin liyafar jajiberin aurenta ya matukar birge jama'a
  • Kamar yadda hotuna da bidiyoyin shagalin suka nuna, bikin ya kankama inda kuma ya dauka kala da shagulgula kala-kala
  • Surayya, diyar tsohon gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido, da angonta Yazid, kwamishinan kasuwanci na jihar Zamfara zasu zama daya a cikin ranakun karshen makon nan

Jigawa - Biki yayi biki kuma shagali ya kankama yayin da Surayya Sule Lamido ke shirin amarcewa da angonta Yazid, kwamishinan kasuwani na Zamfara a cikin kwanakin nan.

Kamar yadda hotunan shagalin suka fara nunawa, an fara ne da fitar da hotunan kafin biki, hotuna da bidiyoyin sanya lalle suka biyo baya sannan hotuna da bidiyoyin liyafar cin abincin dare suka fito.

Surayya and Yazid
Hotuna da Bidiyoyi: Shigar alfarmar da Surayya Sule Lamido Tayi a Liyafar Jajiberin Aurenta ya Kayatar. Hoto daga @theweddingcruize
Asali: Instagram

A hotuna da bidiyoyin da Legit.ng ta tattaro na liyafar cin abincin daren, kyakyawar amaryar ta bayyana cike da shigar alfarma da kasaita wacce ta dace da tsarinta.

Kamar yadda hotuna da bidiyoyin da @theweddingcruize suka nuna, amarya Surayya da angonta sun yi shigar jajayen kaya inda suka birge jama'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba wannan kadai ba, yadda rigar Surayya ke jan kasa daga baya ya matukar birge 'yan mata balle masu shirin amarcewa.

Hotunan kafin biki da Kati: 'Dan sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero da Dalleliyar amaryarsa

A wani labari na daban, birnin Sokoto zai dauka manyan baki inda ake sa ran zai cika dankam da jama'ar da zasu halarci daurin auren 'dan Sarkin kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, Kabiru Aminu Bayero da dalleliyar amaryarsa Aisha Ummarun Kwabo.

Tuni dai shirin wannan bikin na 'yan gata ya kankama inda har aka yi hotunan kafin bikin na amarya da ango cike da izza tare da bayyanar al'adun sarauta.

A hotunan da @fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga jinin sarauta tare da zukekiyar amaryarsa sun cakare gwanin sha'awa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel