Tsaro: Gwamatin Sokoto ta Tumbuke Hakimai 15, An Canzawa Wasu Masarautu

Tsaro: Gwamatin Sokoto ta Tumbuke Hakimai 15, An Canzawa Wasu Masarautu

  • Gwamatin jihar Sakkwato ta sanar da cire rawanin hakimai 15 a jihar bisa laifukan taimakawa ci gaban rashin tsaro a jihar
  • Ana zargin wasu hakiman da rashin biyayya da ladabi ga gwamanati da kuma cinye filayen jama'a haka kawai da kuma rashin da'a
  • Gwamatin ta kuma cire wasu daga hakiman da tsohuwar gwamnati ta nada, tare da sauyawa wasu masarautu a cikin jihar Sakkwato

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto-Gwamnatin jihar Sakkwato ta sauke masu rike da sarautun gargajiya guda tara bisa laifuffukan hannu a cikin rashin tsaro da cinye filayen jama'a, da rashin biyayya ga gwamnati.

Kara karanta wannan

Yayin da ake zarginsa da sulalewa da Yahaya Bello, Gwamna ya roki Tinubu alfarma

Hakiman da aka sauke sun hada da na Unguwar Lalle, da Yabo, da Wamakko, sai Tulluwa, Ilela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu da Giyawa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ahmed Aliyu Sokoto
Gwamnatin jihar Sokoto ta tsige hakimai 15 Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto (Facebook)
Asali: Facebook

Sarakunan da ka tsige a Sokoto

A sanarwar da Abubakar Bawa, mai magana da yawun gwamna Ahmed Aliyu, ya fitar, ya ce gwamnatin ta kori hakimai guda shida da tsohuwar gwamnatin jihar ta nada saboda al'umma ba sa sonsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka sauke sun hada da Marafan Tangaza, Sarkin Gabas, Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun 'yar Tsakkuwa, Sarkin Tambuwal da Sarkin Torankawa.

Sakataren labaran ya ce gwamnatin na bincike hakiman garin Isa, Kuchi, Kilgori da Gagi.

An bar wasu sarakunan Sokoro kan kujerunsu

Rahoton da Leadership News ta wallafa ya nuna ba dukkanin masu sarautun gargajiyar aka sauke daga mukamansu ba.

Kara karanta wannan

Taushen Fage: Al'adar cin nama da sada zumunta da ta shekara sama da 100 a Sakwaya

An sauyawa babban mashawarci a fadar Sarkin Musulmi, Sarkin Yakin Binji wuri zuwa Nabunkari, yayin da aka mayar da hakimin Sabon Birni zuwa Gatawa.

Su kuma hakiman da aka bari a mukamansu sun hada da shugaban Sokoto, Alhaji Aliyu Abubakar III, Barayar Zaki Alhaji Ibrahim Dauki Maccido, Sarkin Arewan Salame Abubakar Salame, da Sarkin Yamman Balle Aminu Bello.

Sauran sun hada da hakimin Sarkin Gabas Dandin Mahe Mahmoud Yabo, da Sarkin Gabas Ambarura Muntari Tukur Ambarura da Sarkin Gabas Rarah Malam Isa Rarah.

Gwamnatin ta ce an mayar da Sarkin Rafin Gumbi AbdulKadir Mujeli kujerarsa, yayin da aka tsare hakiman Tsaki da Asare.

An zargi sarakuna cikin rashin tsaro

Mun kawo mu ku yadda wani mai sharhi, Sani Shinkafa ya zargi sarakunan gargajiya da cewa suna da hannu cikin rashin tsaron da ke addabar jihar Zamfara.

Ya ce masu rike da sarautun gargajiya da jami'an tsaro, likitoci da masu safarar kwayoyi na amfana sosai da rashin tsaron da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel