Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

  • Wani dattijon ya wanke wasu saurayi da budurwa da ya ritsa suna tadi a mota mai duhun gilashi, da dare kuma a lungu mai duhu
  • Kamar yadda dattijon mai dattako ya bayyana, har jikoki garesa kuma hakan yasa sai ya tanka tunda ya ga ana yin abinda ya saba wa shari'a
  • Ya cashe matashin inda yake kwatanta masa da idan kanwarsa ce, zai so a dinga irin wannan tadin da ita?

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani fusattacen dattijo ya yi wa wani matashi tatas tare da budurwar da ya gani suna tadi a mota, cikin duhu kuma a lungu.

Kamar yadda dattijon ya bayyanawa matashin hakan bai dace ba a addinance kuma sabawa hanyar neman aure ce kai tsaye, kamar yadda @northern_blog ta wallafa.

Bidiyon da har yanzu Legit.ng bata san a inda aka nade shi ba, ya bayyana cike da duhu, ba a ganin fuskar saurayin balle budurwar saboda alamu na nuna da dare ne lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Wani Dan Najeriya Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Budurwar Sa Ta Nemi Auren Sa Da Kyautar Tsaleliyar Mota

A cewar dattijon mai dattako, a haka samari ke bata 'yan mata tare da cin musu mutunci. Idan kuwa neman aurenta saurayin yake son yi, kamata yayi ya nemi danginta a san matsaya ba ya rabo ta da gidan iyayenta ba ya kai ta lungu, cikin mota ga dare ana tadi.

A kalaman dattijon mai hangen nesa:

"Ni ina da jikoki, haka muke saboda mu gyara unguwar mu, mu taimaki kanmu da kanmu. Haka ake soyayya? Su bata mana ku a banza da wofi, su wulakanta mana ku, a dinga cin mutuncinmu, kun mana adalci?

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yanzu kai in kana da kanwa uwa daya uba daya, sai ka ga mutum da tinted glass ya zo wurin kanwarka a rufe, a bayan lungun wasu? Ka yi wa kanka adalci? Za ka ji dadi a yi wa kanwarka uwa daya uba daya haka?

Kara karanta wannan

“Mace Daya Ba Za Ta Iya Da Wayona Ba”: Dattijo Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Magantu A Bidiyo

"In aure kake so bisa sunnar Annabi Muhammadu, ka nemi 'yan uwanta, nemi ahalinta, me ya kamata a yi? Amma ba da daddare ba. Ta bar gidan ubanta ta taho lungu, nan lungun ubanta ne? Nan gidan ubanta ne?"

Soyayya gamon jini: Tsoho mai shekaru 93 yayi wuff da budurwarsa mai shekaru 88

A wani labari na daban, wata amarya da angonta sun tabbatar da cewa, soyayya ruwan zuma ce a yayin da suka daura aure duk da yawan shekarunsa.

Ba su yarda cewa tsufa za ta hana su komai ba, sun nemi abokan rayuwarsu, wadanda zuciyarsu ke kauna da kuma wanda suke fatan kare rayuwarsu da shi.

Masoyan junan duk da tsofaffi ne, sun bayyana wurin daurin auren rike da hannayen junansu kuma suna bayyana cewa sun samu soyayya a lokacin da basu taba tsammani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel