Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, An yi wa Addininsa Barazana

Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, An yi wa Addininsa Barazana

  • Kungiyar CCN ta mabiya Katolika tana so a hukunta Simon Bako Lalong kan kalaman da ya yi
  • Shugaban CCN na kasa, Dr. Ben Amodu ya zargi Gwamnan da bata sunan coci da na Fafaroma
  • Kiristoci suna so Gwamnan ya bada hakuri ko a hana shi zuwa coci a kan batun yi wa APC kamfe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Plateau - Wasu mabiya darikar katolika a addinin kiristanci, sun bukaci a dakatar da Gwamna Simon Bako Lalong daga shiga cocinsu a fadin Najeriya.

A ranar Alhamis, 11 ga watan Agusta 2022, Daily Trust ta rahoto cewa Fastocin sun hurowa Simon Bako Lalong saboda yana tare da APC a zaben 2023.

Mai girma Simon Bako Lalong ya amince ya zama shugaban yakin neman zaben Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan Arewa: Kamata ya yi Shettima ya hakura da takara da Tinubu saboda dalilai

Ganin dukkanin wadanda APC ta ba tikiti musulmai ne, wasu suka bada shawarar ka da Gwamnan na Filato ya karbi wannan tayin da aka yi masa.

Baya ga karbar matsayin Darekta Janar na yi wa jam’iyyar APC kamfe, an ji Simon Lalong yana cewa Fafaroma bai fada masa cewa ya yi kuskure ba.

Kamar yadda jaridar Tribune ta fitar da rahoto, kawo maganar Fafaroma a cikin siyasar Najeriya da Gwamnan ya yi, ya fusata malaman addinin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lalong
Kaddamar da Lalong a matsayin DG a Aso Villa Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Rahoton yace Fastocin sun yi tir da Simon Lalong na cusa coci da Fafaroma a kazantar siyasa, suka zargi Gwamnan da neman yaudarar mutane.

Ra'ayin kungiyar CCN

Shugaban wata kungiya ta Fastoci mai suna CCN, Ben Amodu ya kira taron manema labarai a Abuja a jiya, yace ya zama wajibi Gwamnan ya bada hakuri.

Kara karanta wannan

Rikici: Kiristocin APC a Arewa sun ta da hankali, dole a kwace tikitin Shettima a ba su

Dr. Ben Amodu yake cewa akwai bukatar Lalong ya fito fili, ya nemi afuwar cocin katolika da kuma Fafaroma domin kalamansu sun wuce gona da iri.

A cewar shugaban kungiyar ta CCN, bai dace a matsayinsa na wanda ya san darajar cocin katolika, Gwamnan na Filato ya fito yayi irin wannan katabora ba.

Amodu yace babu ruwan coci da harkar siyasa, don haka babu dalilin da za a nemi cin mutuncin mutum mai kololuwar daraja a addininsu irin Fafaroma.

A wani jawabi da Mai girma gwamnan ya fitar, ya wanke kan sa daga zargin da ake yi masa. Gwamnan yace ko kadan bai nufi cin mutuncin Fafaroma ba.

Wike ya je kotu

An samu rahoto a yau cewa Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya yi watsi da batun sulhu a PDP, ya tafi gaban Alkali yana neman zama ‘Dan takaran Jam’iyya.

Bisa dukkan alamu, abin da ya faru wajen tsaida ‘Dan takara a PDP ya yi wa Wike ciwo, ya maka PDP, INEC, Aminu Tambuwal da Atiku Abubakar a Kotu.

Kara karanta wannan

Atiku v Wike: Barakar Cikin PDP Ta Yi Zurfi, Jam’iyya Ta Gagara Yin Muhimmin Taro

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel