Wani Dan Najeriya Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Buduwar Ta Nemi Auren Sa Da Kyautar Sabuwar Motar

Wani Dan Najeriya Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Buduwar Ta Nemi Auren Sa Da Kyautar Sabuwar Motar

  • Bidiyon wata mata 'yar kasar Kenya da ta nemi saurayin ta dan Najeriya ya aureta ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta
  • A cikin faifan bidiyon da ake ta yadawa, matar ta ba shi kyautar mota sannan ta durkusa a gwiwa daya domin neman aurensa
  • Saurayin ya fashe da kuka a lokacin da ta nemi auren sa, bayan an gashi yana yawo a cikin motar wanda ya nuna ya amince zai aure ta

Kenya - Wata mata ‘yar kasar Kenya da take soyayya da wani dan Najeriya, ta nemi auren sa a wani yanayi mai ban mamaki. Rahoton Legit.NG

Kyakkyawar matar ta dukursa a gaban saurayin ta inda ta mika mishi zobe mai matukar tsada tare da makulin sabuwar mota a ranar ta da roke shi ya aure ta.

Kara karanta wannan

“Mace Daya Ba Za Ta Iya Da Wayona Ba”: Dattijo Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Magantu A Bidiyo

Wani irin yanayi yasa saurayin ya fashe da kuka yana mika mata yatsan sa don ta saka zoben wanda ya nuna ya amince da aurenta.

Kenya
Wani Dan Najeriya Ya Fashe Da Kuka Lokacin da Yar Kenya To Nemi Auren Sa Da Kyautar Sabuwar Motar FOTO @africanvsfood
Asali: UGC

Faifan Bidiyon da dandalin @africanvsfood on TikTok yasa mutane da yawa suna ta tofa albarkacin bakin su akan lamarin

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mai suna @felestus a shafin TikTok ya ce, haka bazai taba faruwa dashi ba, saboda shi ba mai matance zuciya bane.

Wata mai suna @shayanjebet4 ta ce hakan na iya faruwa da zarar aikin boka ya wuce gona da iri, namiji ya kamata yayi haka.

yanzu bayan kwana biyu sai ka ga yafara diban yan mata a cikin motar irin wannan soyayya akwai bakin ciki inji ta.

Ga Bidiyon A Kasa

Sanusi: Na Gargadi Gwamnatin Buhari Cewa Manufofinta Za Su Lalata Tattalin Arzikin Najeriya

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

A wani labari kuma, Jihar Legas - Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa sai da ya gargadi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa manufofinta na tattalin arziki za su lalata arzikin Najeriya. Rahoton THIS DAY

Sanusi ya kuma koka da halin da kasar ke ciki, yana mai cewa Najeriya ba za ta sami cigabar da yakamata ba muddin masu rike da mukaman gwamnati basu dauki aikinsu da kima ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel