Hanyoyi 5 na warkar da ciwon basir

Hanyoyi 5 na warkar da ciwon basir

Idan kana da dauke da cutar basir, kuma baka son kashe kudi akan aikin tiyata, toh ka gwada bin wadannan hanyoyin. Suna aiki matuka.

Hanyoyi 5 na warkar da ciwon basir

 

Hanyoyi 5 na warkar da ciwon basir

Alamun mutum na dauke da cutar basir: mutum zai rika fama da wadannan matsaloli

-kaikayi da bacin rai

-fitar jinni, amma ba tare da anji zafi ba

-ciwon jiki da rashin sakewa

-kumburar dubura

-fitan curi ko dunkule a dubura

Abubuwan dake kawo basir suna da dama, amma dai duk asalin su guda. Idan Jijiyoyin dake dubura suka wahala. Amma mafi yawancin sanadin basir sune:

-haihuwa

-kiba

-fitan bayan gida da kyar

-yawan cin abinci mai maiko

-saduwa ta dubura

-dauan ciki

Wadannan hanyoyin na kawar da kamuwa da cutar basir, koma wani iri ne.

1. Cin abinci mai gina jiki

Ana son mutum dinga cin kayan hatsi da kayan marmari da kuma ganyayyake don sune masu wanke tumbi kuma suna taimakawa wajen nika abinci a cikin ciki.

Suna kawar da wahalar yin bayan gida. Sa’annan sai su kawar da alamun basir.Bugu da kari ana so mutum ya rage cin nau’in abinci mai maiko da kuma jan nama. Ireiren abincinnan na janyo basir.

2. Yawaita shan ruwa mai kyau, domin yana wanke hanji kuma yana taimakawa wajen nika abinci a ciki.

3. Yawan ci da shan sinadari bitamin C

Sinadarin Bitamin C na kara wa jijiyoyi karko da lafiya. Don haka nau’o’in abinci irin su lemun tsami, tuffa da timatir na taimakawa wajen magance basir. Ya kamata kowa ya ringa yin wannan, har a masu juna biyu.

4. Motas Jiki.

Yawan zaman dabano ba tare da motsa jiki ban a janyo wahalan tsuguno. Motsa jiki na taimakawa wajen baiwa jijiyoyi da ciki kansa koshin lafiya. Motsa a jiki a kullum zai magance matsalar cutar basir. Amma banda cin karfe.

5. Wanka da rowan dumi

Idan kaan bukatan kawar da alamun basir kamar su ciwon jiki da kaikayi, toh kayi wanka da rowan dumi hadi da ganyayyakin gargajiya. Hakan zai saukar da ciwon jikin kuma ya tsaida kaikayin. Kuma zai hana kumburi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel