Bikin Sallah: Abubuwan da Ake So Musulmi Ya Yi a Ranar Hawan Idi

Bikin Sallah: Abubuwan da Ake So Musulmi Ya Yi a Ranar Hawan Idi

Eid al-Fitr ‘Idin buda baki’ ko 'karamar Sallah', da kuma Eid al-Adha 'Idin layya' ko ‘babbar Sallah’, na daga cikin bukukuwa mafi girma ga Musulmi a kowace shekara.

Ranar hawan Idi ita ce ranar da musulmi a duk fadin duniya suke jiran zuwanta. Muna dauke da sababbin tufafi, muna dafa abinci masu daɗi, kuma muna bikin Idi tare da masoyanmu.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abubuwan da ake so Musulmi ya yi a ranar Sallah
Ana so Musulmi ya yawaita kabbara tun daga jajibirin Idi tare da yin wanka a ranar Sallah. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Akwai wasu abubuwa 8 da ake so Musulmi ya yi a ranar hawan Idi domin sanya wannan ranar ta zama na musamman ga danginku da ku kanku, kamar yadda shafin Halal Trip ya wallafa.

1. Yawaita yin 'Takbir'

Daya daga cikin hanyoyin da musulmi suke gudanar da Idi shine ta hanyar yawaita yin kabbara tun daga jajibirin Idi (bisa ga ganin wata) har sai an fara sallar idi da safe.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Jami'in dan sandan da ya yi barazanar sheke farar hula da bindiga ya shiga hannu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kila za ku ji ana rera kabbara a gidajen rediyo, talabijin da masallacin anguwarku, da sauran wurare amma zai fi ku rika furtawa da kanku, kuma ba lallai ne ku yi hakan a bayyane ba.

Ana yin kabbarar hawan idin kamar haka;

“Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, laa ilaaha ill-Allah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, wa Lillaahi’l-hamd.”

2. Wanka da saka tufafi mai kyau

Yin wankan Idi mustahabbi ne (amma mai karfi) ga dukkanin Musulmi. Ana yin wankan ne a safiyar ranar Sallah kafin a tafi masallacin Idi.

Hakazalika ana so mutum ya saka sababbin tufafi ko kuma masu kyau. Ga maza da mata ana so kowa ya kure adakarsa a wannan rana, rahoton Daily Trust.

3. Tafiya zuwa sallar Idi

Sallar Idi tana dauke da raka'a biyu, ta farko tana dauke da takbirai bakwai, ta biyu kuma biyar. Ana yin huduba ne bayan an idar da Sallah.

Kara karanta wannan

Watanni 2 da maganar komawa APC, Abba ya dauko binciken Ganduje da iyalinsa

Haka nan sunnar Annabi SAW ta ce yana da kyau a yi sallar Idi a cikin jama'a kuma a babban fili. Haka nan sunna ne ka bi hanyoyi daban-daban a yayin zuwa sallar Idi da kuma komawa gida.

4. Cin abinci mai dadi

Sunna ita ce ka yi buda baki da sassafe da dabino kafin ka tafi sallar Idi, amma kuma kana iya cin wani abu daban.

"Annabi (SAW) ba ya zuwa (wurin Sallah) da safe a ranakun Idi har sai ya ci dabino, kuma ya kasance yana cin adadin da ba a rabawa biyu."

- [Sahih-Al-Bukhari]

Da zarar an dawo daga sallar Idi, cin abinci mai dadi na daya daga cikin hanyoyin da Musulmi ke gudanar da murnar bikin Sallah.

5. Bayar da Zakka

Zakka tana daya daga cikin rukunan Musulunci, kamar yadda azumi yake. Daga cikin abubuwan da ya kamata a tuna da ranar Idi shi ne tabbatar da cewa kun cika farillai da bayar da zakka.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi martani kan lafta masu haraji a wani titin jihar Legas da Calabar

Goni Abubakar Sa'idu Musa Funtua ya ce ana so Musulmai su fitar da zakka fidda kai a lokacin da Ramadan yazo karshe ga mutanen da basu da hali na abincin da za yi buda baki da shi.

Malamin ya ce akan fara bayar da zakkar fidda kai tun ana saura kwanaki biyu ayi biki Sallah, amma wajibcin lokacin bayarwa shi ne kafin a dawo daga sallar Idi.

"Ana bayar da nau'ikan abinci da aka fi ci, kamar shinkafa, gero, dawa, masara, alkama da dai sauransu."

- A cewar Malamin.

Don haka, ku tabbata kun fitar da zakkarku domin taimakawa marasa galihu kafin zuwan ranar Idi.

6. Bada sadaqa da kyauta

Duk da cewa bayar da zakka wajibi ne, amma bayar da sadaka ba wajibi bane. Amma yana da kyau a bayar domin Sadaka tana ɗaya daga cikin ayyuka mafi lada da Musulmi zai aikata.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Yayin da kuke da halin dinka kyawawan sabbin tufafi, ku dafa abinci mai kyau, akwai bukatar ku tuna da waɗanda ba su da hali kamar ku.

Ku taimaka musu ta hanyar samar musu da abinci a ranar Idi, bada sabbin tufafi ga yaran, ko dukkanin wani abu da zai amfane su.

7. Ziyarci 'yan uwa da abokan arziki

Wani muhimmin abu da ya kamata ku yi don bikin Idi shi ne ziyartar abokai, dangi, da makwabta. Ku gaishe su da sakin fuska, a kuma yi musu fatan ‘an yi sallar Idi lafiya.'

Daya daga cikin abubuwan da za a rika tunawa da ranar Idi shi ne tabbatar da ziyartar marasa lafiya da tsofaffi, ko ziyartar makabarta ga maza.

8. Dorewa da ibada

Ramadan lokaci ne da dukkanmu muka himmantu wajen ganin mun kasance a kan kyawawan dabi'unmu, a matsayinmu na Musulmi da 'yan Adam baki daya.

Haƙiƙa, ba lallai ne kuma ka ba da lokaci mai yawa don yin addu'a, karatu, zikiri da ibada ba kamar yadda ka yi a cikin Ramadan, amma kar kuma ka janye daga yin ibada.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: Wurare 5 masu kayatarwa da ya kamata ku ziyarta a Kaduna

Bikin Sallah: An tsaurara tsaro a Yobe

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Yobe tare da hadin guiwar jami'an tsaro sun shirya wa bikin karamar Sallah.

Gwamna Mai Mala Buni ya ce an jibge jami'an tsaro a lungu da sako na jihar domin tabbatar da cewa an gudanar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel