Kano: 'Yan Sanda Sun Kama Wani Kan Sace Dan Makwabcinsa Tare Da Neman N100m Kudin Fansa

Kano: 'Yan Sanda Sun Kama Wani Kan Sace Dan Makwabcinsa Tare Da Neman N100m Kudin Fansa

  • Rundunar yan sandan Kano ta kama wani Musa Isah, mai shekara 30, mazaunin kauyen Makadi kan zargin garkuwa da dan makwabcinsa tare da neman Naira miliyan 100 kudin fansa
  • Bayan kama shi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi da wani abokinsa ne suka hada baki kuma da farko sun nemi N100m amma daga bisani suka rage zuwa N2m
  • Rundunar yan sandan na Kano ta ce ana zurfafa bincike a kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Rundunar yan sandan Jihar Kano ta kama wani Isah Musa, dan shekara 30 mazauna kaunyen Makadi a karamar hukumar Garko kan sace dan makwabcinsa tare da neman a biya N100m kudin fansa, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Taswirar Jihar Kano.
Kano: 'Yan Sanda Sun Kama Wani Kan Sace Dan Makwabcinsa Tare Da Neman N100m Kudin Fansa. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin yan sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa a ranar Alhamis, da ya rabawa manema labarai ya ce da farko wanda ake zargin ya nemi N100m daga baya ya rage zuwa N2m.

Sanarwar ta ce: "A ranar 31/07/2022 misalin karfe 0800hrs, wani mazaunin kauyen Makadi, karamar hukumar Garko a Jihar Kano yace an tuntube shi a tarho an masa barazanar ya biya N100m, idan ba haka ba za a sace shi ko daya cikin yayansa. Kuma, sunyi ciniki sun yarda zai biya Naira miliyan 2.
"Bayan samun korafin, mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP, Abubakar ya umurci tawagar yan sanda karkashin jagorancin SP Aliyu Muhammad Auwal, na sashin yaki da garkuwa su binciko wanda ake zargin su kama shi(su).
"Tawagar sun kama aiki nan take, bayan samun bayannan sirri suka bi sahu suka kama wanda ake zargin, wani Isah Musa, mai shekara 30, makwabcin mutumin da ya shigar da korafin.

Kara karanta wannan

Dan Kungiyar Asiri Ya Dana Wa Kansa Harsashi A Lokacin Da Ya Ke Kokarin Sarrafa Bindiga

"Binciken farko da aka fara yi, wanda ake zargin ya amsa cewa wanda abin ya faru da shi makwabcinsa ne kuma mahaifin abokinsa.
"Ya hada baki da wani abokinsa wanda ke zaune can wajen jihar ya rika tattaunawa a madadinsa.
"Sun nemi N100m amma daga baya suka rage zuwa N2m. Za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike,"

DCP ya gode wa mutanen Jihar Kano saboda cigaba da bada gudunmawa da hadin kai.

'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu

A wani rahoton, Mustapha Imam, daya daga cikin mutanen da yan bindiga suka sace jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja ya ce ya yi wa yan bindiga magani a lokacin da ya ke tsare a hannunsu.

A wani bidiyon da Tukur Mamu, mawallafin Desert Herald wanda ya taimaka wurin tattaunawa don ganin an sake su, fasinjan ya bayyana zamansa a hannun yan bindigan a matsayin 'lamari matukar muni'.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

Imam, wanda ma'aikaci ne a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce ba zai yi wa makiyinsa fatan shiga halin da ya tsinci kansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel