Za a fuskanci ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba a Najeriya, NiMet

Za a fuskanci ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba a Najeriya, NiMet

  • Hukumar kula da yanayi ta NiMet ta sanar da cewa za a fuskanci ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba
  • Kamar yadda shugaban hukumar, Farfesa Mansur Bako Matazu ya sanar, wannan ya shafi sauyin yanayi a duniya
  • Ya shawarci jama'a da ke kusa da wuraren da aka saba ambaliyar da su hanzarta tattara komatsansu su bar wurin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya zata fuskanci gagarumar ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba, kamar yadda hukumar kula da yanayi, NiMet ta tabbatar.

Shugaban NiMet, Farfesa Mansur Bako Matazu, ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin na Channels TV a ranar Litinin.

Professor Bako Matazu
Za a fuskanci ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba, NiMet. Hoto daga 21stcenturychronicle.com
Asali: UGC

Yace cibiyar ta bada shawarwari daban-daban akan ambaliyar ruwa wanda 'yan Najeriya suka ki kiyayewa.

Farfesa Matazu yace: "Za a samu karin yawan ruwan sama a watanni biyu masu zuwa. Zai fi yawa a watannin Yuli, Augusta da Satumba. Za mu fuskanci karin ambaliyar ruwa."

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyo: Dankareriyar daham din da Fatima Shettima ta saka wurin wushe-wushe ya dauka hankali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan abu ne da duniya baki daya ya kamata ta damu da shi saboda yana da alaka da sauyin yanayi kuma akwai abubuwan dake kawo shi.

"Don haka, za a samu karfin ambaliyar ruwa kuma muna shawartar MDAs ballantana a matakin jihohi da kananan hukumomi da su shawarci mutanen da ke kusa da wuraren da ake samun ambaliya ko za a iya samu da su tattara su bar wuraren," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel