Yanzu-Yanzu : Kotu Ta Bada belin Dakataccen Akanta-Janar

Yanzu-Yanzu : Kotu Ta Bada belin Dakataccen Akanta-Janar

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Daktaccen Babban Akanta Janar na Tarayya, Idris Ahmed
  • Alkalin kotu ya zarrtar da hukuncin ba da belin Ahmed bisa hujjar cewa ba a tabbatar da zargin da ake tuhumar sa ba
  • Tsohon Akanta Janar Ahmed Idirs Tare da wadanda ake tuhuma ba za su bar birnin Abuja ba sai da izinin kotu

Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Babban Akanta Janar na Tarayya, Idris Ahmed tare da wadanda ake tuhumar su bisa sharuddan da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC ta bayar. Rahoton Channels TV

Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Adeyemi Ajayi ya ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ba za su bar birnin tarayya ba, kuma idan sun so sai su nemi izinin kotu ko kuma a soke belinsu.

Kara karanta wannan

2023: Cocin Anglican Ta Fada Wa Kiristoci Abin Da Za Su Yi Game Da Tikitin Musulmi Da Musulmi Da APC Ta Yi

Kotun ta kuma bayyana cewa wadanda ake tuhumar za su rattaba hannu kan yarjejeniyar cewa za su bi ka’idojin belin da EFCC ta gindaya musu.

ahemd idris
Yanzu-Yanzu : Kotu Ta Bada belin Dakataccen Akanta-Janar
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai shari’a Ajayi ya kuma ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar kada su sayi fasfo na daban har sai an kammala shari’ar, bayan sun ajiye fasfo dinsu na asali ga hukumar.

Alkalin kotun ya zartar da hukuncin ne bisa hujjar cewa har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba.

Kotun ta kuma bayyana cewa, bisa tsarin doka, wadanda ake tuhumar suna da damar bayar da belinsu duk da zargin da ake musu, tun da mai gabatar da kara bai bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun aikata ba daidai ba a lokacin da suke hannun EFCC.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya yi martani kan barazanar tsige shi da sanatocin PDP suka yi

An fara shari'a kai tsaye bayan yanke hukuncin neman beli.

Gwamna Zulum Ya Yiwa Almajirin Borno da Ya Kirkiri Tarakta kyautar N5m

A wani labari kuma, Gwamna Babagana Umara Zulum a jiya, Laraba, ya bayar da kyautar Naira miliyan biyar (N5m) don tallafawa fasahar wani almajiri mai hazaka a jihar Borno, wanda ya kera injin din garma.

Galibi ana haɗa garma da tarakta ne, da wasu na’urorin sufuri, ko kuma a jan su da hannu a gonaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel