Bidiyon ciki da wajen jirgin saman da biloniyan Najeriya ya siya N63 biliyan ya gigita jama'a

Bidiyon ciki da wajen jirgin saman da biloniyan Najeriya ya siya N63 biliyan ya gigita jama'a

  • Fitaccen biloniyan Najeriya, Prince Arthur Eze, ya siya katafaren sabon jirgin sama na kanshi wanda ya kara cikin ababen hawansa
  • Wani bidiyonsa da ya yadu a dandalin sada zumunta, an nadi yadda mashahurin mai kudin ke duba cikin jirgin saman tare da wasu ma'aikatansa
  • Rahotannin sun tabbatar da cewa, hamshakin mai arzikin ya siya jirgin saman kirar Gulfstream G450 kan kudi har N63 biliyan

Fitaccen biloniyan 'dan kasuwan Najeriya, Prince Arthur Eze, ya samu karbar katafaren jirgin saman da ya siya kirar Gulfstream G450.

A wani bidiyo da ya yadu a dandalin sada zumuntar zamani, kwararren 'dan kasuwan kuma mashahurin mai arzikin ya bayyana ciki da wajen jirgin saman yayin da yake zagaya shi tare da ma'aikatansa.

Prince Arthur
Bidiyon ciki da wajen jirgin saman da biloniyan Najeriya ya siya N63 biliyan ya gigita jama'a. Hoto daga @mufasatundeednut
Asali: Instagram

Arthur Eze shi ne mamallakin Atlas Oranto Petroleum, daya daga cikin manyan kamfanonin hakar man fetur masu zaman kansu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

A yanzu haka, kamfaninsa yana da lasisin hakar mai 22 a sassan 12 na nahiyar Afrika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bidiyo dake bayyana 'dan kasuwan yana zagaya cikin jirgin saman, an ga ma'aikatansa na biye da shi.

@mufasatundeednut ne ya wallafa bidiyon a shafinsa na Instagram inda aka ga ya rubuta:

"Prince Arthur Eze Ozoigbondu Global ya siya dallelen sabon jirgin saman 'dan yayi, American G450 Gulfstream mai darajar $150,000,000."

'Yan Najeriya sun yi martani kan jirgin saman

Dapublicist cewa yayi: "Wannan ai tsohon mai kudi ne... Biloniya ne tun kafin a haife ni. Ina taya shi murna."
Djbign yace: "Wannan mutumin yana da kazaman kudi tun kafin a haife ni. Ni kuma har yanzu shiru babu labari... Ina taya ka murna ran ka shi dade."
Suma_Marie tace: "Ku taya ni murna nima, na siya kan cajar waya mai darajar 1,500 a wannan matsin da ake ciki, babu sauki gaskiya."

Kara karanta wannan

Kamfanin Dubai Mai Ma’aikata 61,000 Ta Karrama Dan Najeriya A Matsayin Gwarzon Wata

Reigns Ann ta kara da: "Fitattun nan sun fara tururuwar yi masa murna da wata manufa ta daban."
Queenofdsun tace: "Akwai kudi a hannun wasu mutane fa. Ni su kira ni domin kawata cikin jirgin saman."

Bayyanar bidiyo da hotunan motar jaruma Nafisa Abdullahi ta N30m ta dauka hankali

A wani labari na daban, wasu sabbin bidiyo da hotuna na jaruma Nafisat Abdullahi tana shagalinta da tsadajjiyar mota ya dauka hankulan jama'a masu tarin yawa.

Ba kuwa komai bane ya dauka hankalin jama'a ba illa zukekiyar mota da aka ga jarumar ta fizgo wacce ta kasance 'yar yayi wacce ba kowa ke iya hawanta ba sai wane da wane ke iya hawan irinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel