Yadda Aka Haifi Jarirai 27,490 Cikin Watanni Uku A Jihar Kano

Yadda Aka Haifi Jarirai 27,490 Cikin Watanni Uku A Jihar Kano

  • Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na Kano ta bayyana cewa cikin watanni uku kacal an haifi jarirai 27,490 a fadin jihar
  • Shugaban hukumar dake kula da asibitoci ta jihar Kano, Nasiru Alhassan, ya ce wannan sune adadin da aka haifa a asibiti amma suna iya fin haka
  • Gwamnatin ta Kano ta bukaci kungiyoyin fararen hula da su ci gaba da tallafa wa bangaren lafiya

Kano - Gwamnatin jihar Kano a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli, ta bayyana cewa an haifi jarirai 27,490 a cibiyoyin kiwon lafiya da ke fadin jihar.

Babban daraktan hukumar dake kula da asibitoci ta jihar Kano, Nasiru Alhassan, ne ya bayyana hakan yayin da yake kaddamar da shirin rabon kayan kiwon lafiya ga asibitoci a jihar.

A wajen taron, Mista Alhassan, wanda ya samu wakilcin shugaban likitocin gwamnati, Sulaiman Hamza, ya ce daga cikin jariran 27,490 an haifi 681 ta hanyar tiyata, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dangote, Dantata da Jerin Kanawa 8 da ke cikin Sahun Masu kudin Najeriya

Ganduje
Yadda aka haifi jarirai 27,490 cikin watanni uku a jihar Kano Hoto: Guardian.ng
Asali: Twitter

Amma adadin wadannan yara da aka haifa a jihar cikin wadannan watanni da ake magana na iya fin 27,490. Jihar Kano na daya daga cikin wurare da masu ciki masu fiya zuwa asibiti ba a lokacin haihuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kaso 21.5 cikin dari wato biyu cikin 10 na haihuwa ne kwararrun ma’aikatan asibiti ke karbar haihuwarsu a jihar Kano, kamar yadda wani rahoto ya bayyana a 2020.

Hukumar lafiya ta Najeriya ce ta gudanar da binciken kuma ta zagaya asibitoci 49 a kananan hukumomi 44 na jihar.

Mista Alhassan ya kuma jinjinawa abokan hulda saboda taimakon da suke bawa harkar lafiya a jihar inda ya bukaci kungiyoyin fararen hula da su ci gaba da tallafa wa bangaren lafiya, rahoton Leadership.

Kano na daya daga cikin jihohin da aka fi samun yawan mace-macen jarirai da mata masu juna biyu a Kano a kasar.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, Mun ba Shugaban Kasa Rahoton Fasa Gidan Yarin Kuje inji Minista

Kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana, masu juna biyu 1,025 ne ke mutuwa a cikin 100,000 wajen haihuwa.

Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai A Sabon Bidiyo

A wani labari na daban, mun ji cewa yan makonni bayuan farmakin da aka kaiwa ayarin motocin shugaba Muhammadu Buhari a jihar Katsina, yan ta’adda sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasar na Najeriya.

An dai farmaki tawagar tsaron shugaban kasar a hanyarsu ta zuwa mahaifar Buhari da ke Daura gabannin bikin Sallah.

Mutane biyu sun jikkata a harin wanda aka ce fadar shugaban kasar ta dakile.

Asali: Legit.ng

Online view pixel