Kotu ta Yarda a Binciki ‘Dan takaran APC, Tinubu a kan abin da aka yi a 1999

Kotu ta Yarda a Binciki ‘Dan takaran APC, Tinubu a kan abin da aka yi a 1999

  • Babban kotun tarayya na Abuja ta yi zama a kan karar da aka kaiwa ‘Yan Sanda saboda Bola Tinubu
  • Alkali ya saurari shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1058/2022, ya yarda ayi shari'a da ‘dan takaran
  • Wata kungiya ta ce Bola Tinubu ya aikata laifi, amma ‘Yan Sanda ta ki kai karar shi a gaban kotu

Abuja - A ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli 2022, babban kotun tarayya da ke garin Abuja, ta bada damar ayi shari’a da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a kotu.

Punch ta kawo rahoto da yammacin nan cewa Alkali ya yi na’am da rokon da wata kungiya take yi, na tursasawa ‘yan sanda yin shari'a da Bola Ahmed Tinubu.

Da aka zauna a kotu dazu, Mai shari’a Inyang Ekwo ya amince da bukatar da Incorporated Trustees of Center for Reform and Public Advocacy ta gabatar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Lauyan da ya tsayawa kungiyar, Ugo Nwofor yana zargin ‘dan takaran na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa, ya taba karya alhali akwai rantsuwa a bakinsa.

Za ku iya shigar da kara - Alkali

Kamar yadda dokar kasa ta yi tanadi, Nwofor ya fara neman izinin kotu kafin ya shigar da kara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Inyang Ekwo ya karbi rokon da Nwafor yake yi, ya zartar da hukunci cewa kungiyar ta na da damar da za ta nemi ayi shari’a a kotu da wadanda ake tuhumar.

‘Dan takaran APC
Bola Tinubu da Mai dakinsa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Daily Post a rahoton da ta fitar yau, ta ce Alkalin ya zabi ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin lokacin da kotu za ta zauna domin sauraron wannan kara da kyau.

Incorporated Trustees of Center for Reform and Public Advocacy ta na ikirarin Tinubu ya yi karya a game da takardun makarantansa, wanda hakan laifi ne.

Kara karanta wannan

Musulmi-Musulmi: APC na da boyayyar makarkashiya inji Tsohon Ministan Buhari

Ganin shugaban ‘yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba ya ki daukar mataki na kai ‘dan siyasar kotu, kungiyar ta tashi da kan ta, ta kai maganar gaban Alkali.

Hakan na nufin wannan kungiya za ta iya shigar da kara da kyau a kotu, ta yi shari’a da Tinubu wanda shi APC ta tsaida a matsayin ‘dan takaran shugaban kasa.

Takarar Tinubu da Shettima

An ji labari cewa dauko Kashim Shettima da Bola Tinubu ya yi, ya bar baya da kura a jam'iyyar APC, ana tunani Jiga-jigan Inyamurai suna neman juya masa baya

‘Yan takara da Gwamnoni irinsu Hope Uzodinma, Dave Umahi, Ogbonnaya Onu, Rochas Okorocha sun ki amsa goron gayyata zuwa taron kaddamar da Shettima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel