Manyan Kudu sun yi watsi da APC, Tinubu, sun ki halartar bikin kaddamar da Shettima

Manyan Kudu sun yi watsi da APC, Tinubu, sun ki halartar bikin kaddamar da Shettima

  • Bola Tinubu ya kaddamar da Kashim Shettima a matsayin ‘Dan takaran mataimakin Shugaban kasa a APC
  • Da alama dauko Sanata Kashim Shettima ya fusata wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC mai mulki
  • Kamar an hada baki, kusan duka manyan APC na shiyyar Kudu maso gabas, ba su zo bikin kaddamawar ba

Abuja - Gwamnoni, masu neman takara, da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen Kudu maso gabas ba su iya zuwa wajen taron kaddamar da Kashim Shettima ba.

A wani rahoto da Punch ta fitar a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli 2022, ta nuna manyan ‘yan siyasar yankin sun kauracewa bikin kaddamar da ‘dan takaran.

A cikin wadanda aka gani a wajen taron da aka shirya a cibiyar Shehu Musa Yar’Adua, akwai shugabannin jam’iyyar APC na kasa da wasu Gwamnonin APC.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

‘Yan majalisar NWC a karkashin jagorancin Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore su na wajen. Haka zalika tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.

Jaridar ta ce an ga Godswill Akpabio, Gwamnonin jihohin Ekiti, Borno, Kebbi da Kano; Kayode Fayemi, Babagana Zulum, Atiku Bagudu da Dr. Abdullahi Ganduje.

Wasu sun ki zuwa taron

Amma kusoshin jam’iyyar APC na shiyyar Kudu maso gabas, duk ba su samu zuwa taron ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bikin kaddamar da Shettima
Kashim Shettima da Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Ba a iya ganin fuskokin Ikeobasi Mokelu, Dr. Ogbonnaya Onu, Gwamna Dave Umahi, Sanata Tochas Okorocha da kuma Hon. Chukwuemeka Nwajiuba a wajen ba.

Wadannan ‘yan siyasa su na cikin abokan adawar Bola Tinubu wajen neman tikitin APC na zama ‘dan takarar shugaban kasar 2023 daga bangaren kudu maso gabas.

Me ya yi zafi haka?

Kamar yadda rahoton ya shaida, Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma wanda a baya ya nuna goyon baya ga Tinubu a 2023, bai sa kafansa a dakin taron ba.

Kara karanta wannan

2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata

Ana zargin watakila wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC ba su ji dadin dauko Sanata Kashim Shettima da Tinubu ya yi a matsayin abokin takaran 2023 ba.

Har ‘Yan kungiyar APC Hausa-Fulani Youth Forum a karkashin jagorancin Abdullahi Bilal Mohammadu sun yi zanga-zanga, suna cewa an danne Kiristocin Arewa.

APC ba za ta ci zabe ba - Dalung

Ku na da labari tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung ya fadi ra’ayinsa game da 2023, ya bayyana dalilin Asiwaju Tinubu na dauko Sanata Kashim Shettima.

A cewar Dalung, APC ba tayi wani abin kirki cikin shekaru bakwai ba, sannan ta ki ba Kiristan Arewa takara, ya ce hakan zai jawo jam’iyyar ta sha kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel