'Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari ƙauyukan Ƙatsina, sun kashe mutane

'Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari ƙauyukan Ƙatsina, sun kashe mutane

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai hari kauyuka biyu a yankin ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina da tsakar ranar Talata
  • Mazauma yankunan sun tabbatar da cewa mutane 6 sun rasa rayuwarsu a harin, wasu kuma na kwance a Asibiti
  • Kakakin hukumar yan sanda, SP Gambo Isa, ya tabbatar da kai harin, ya ce tuni dakarun yan sanda suka mamaye yankin

Katsina - 'Yan bindiga da adadi mai yawa sun farmaki ƙauyukan Ruwan Goɗiya da Kwai da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina da tsakar ranar nan ta Talata.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa miyagun sun kashe mutum Shida, sun jikkata wasu da yawa sannan kuma suka tattara shanu da sauran dabbobi suka yi gaba da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jiha, yan sanda sun ce ba zata saɓu ba

An sake kai hari Katsina.
'Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari ƙauyukan Ƙatsina, sun kashe mutane Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, Lawal Kafinta, ya shaida wa jaridar ta wayar Salula cewa yan ta'addan sun kashe mutum ɗaya a ƙauyen Kwai dake maƙwaftaka da Ruwan Godiya kuma suka jikkata wasu da yawa.

A cewarsa, maharan waɗan da suka hana zaman lafiya a wasu garuruwan makwafta sun shiga ƙauyukan kan mashina kuma ana tsammanin sun haura 100.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lawal Kafinta ya ce:

"Eh, maharan sun kashe mutum biyar a ƙauyen Ruwan Godiya da kuma mutum ɗaya a Kwai, sun kuma jikkata mutane da yawa a harin, yanzu da muke magana da ku suna kwance a Asibitin Funtua."
"Lamarin ya faru yau da rana tsakanin ƙarfe 12:00 zuwa 1:00. Ba su shiga garin Faskari ba, sun aikata nufin su nesa da garin inda makiyaya suka saba kiyon su."

Hukumar yan sanda ta tabbatar

Yayin da wakilin jaridar The Nation ya tuntubi kakakin hukumar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da kai hari kauyen Ruwan Goɗiya, inda ya ce:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sace wani babban Basarake a arewa

"Eh dagaske ne, yan ta'addan sun kai farmaki da misalin ƙarfe 1:30 na rana suka kashe mutum 6 kuma suka jikkata wasu Shida."
"Tuni aka garzaya da waɗan da suka jikkata zuwa Asibiti. Haka nan kuma jami'an mu suna can don tabbatar da tsaro."

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sake kai hari Dutsin-ma, sun sace matan aure da kananan yara

Makonni kaɗan bayan kashe kwamandan yankin Dutsinma, yan bindiga sun yi garkuwa da mutum Tara a Shema Quaters.

Maharan sun yi awon gaba da matan aure hudu da kananan yara biyar a harin da suka kai cikin garin Dutsinma ana tsaka da ruwa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel