Nasarawa: Allah ya yiwa babban basaraken Eggon, Bala Angbazo, rasuwa
- Babban basaraken Eggon, Aren Eggon Bala Angbazo, ya kwanta dama a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli
- Basaraken na jihar Nasarawa ya mutu yana da shekaru 89 a duniya bayan ya yi fama da dogon jinya
- Marigayi Anbazo wanda aka nada kan sarauta a ranar 11 ga watan Yulin 1981, ya shafe tsawon shekaru 41 kan kujerar sarauta
Nasarawa - Aren Eggon kuma babban sarkin kabilar Eggon ta jihar Nasarawa, Bala Angbazo, ya rasu.
Galadiman Eggon, Mista James Anbazo, ne ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, a garin Lafia.
Ya bayyana cewa Aren Eggon ya rasu ne a ranar Laraba bayan ya yi fama da dogon jinya. Ya mutu yana da shekaru 89 a duniya, jaridar Daily Trust ta rahoto.
An haifi babban basaraken a yankin Wakama da ke karamar hukumar Nasarawa-Eggon ta jihar a shekarar 1933.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Marigayi Anbazo wanda aka nada kan sarauta a ranar 11 ga watan Yulin 1981, ya rasu bayan shekaru 41 kan karagar mulki, rahoton The Sun.
Allah ya yiwa dan majalisa, Olusegun Popoola, rasuwa
A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya yiwa dan majalisar dokokin jihar Oyo, Ademola Olusegun Popoola, rasuwa.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Popoola ya rasu ne a safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, yana da shekaru 46 a duniya.
Dan majalisar shine ke wakiltan mazabar Ibadan ta kudu maso gabas a majalisar dokokin jihar.
Asali: Legit.ng