Kotu ta yanke wa yan luwadi hukuncin kisa a jihar Bauchi

Kotu ta yanke wa yan luwadi hukuncin kisa a jihar Bauchi

  • Kotun musulunci ta yankewa yan luwadi hukunci kisa ta hanyar jefewa
  • Yan luwadin suna amfanin da kwakwa da dabino wajen yaudarar kananan yara
  • Masu laifin luwadi da kotu ta yankewa hkuncin kisa suna damar daukaka kara cikin wata daya

Jhar Bauchi : Babbar kotun shariar musulunci dake jihar Bauchi ta yanke wa wasu matasa biyu da dattijo hukuncin kisa ta hanyar jefewa ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022. bisa laifin yiwa wasu kananan yara luwadi.

Al’amarin ya faru ne a karamar hukumar Ningi kamar yadda jaridar BBC hausa ta rawaito.

Kotun ta samu mutanen, wanda suka hada da matasa biyu da kuma wani dattijo mai misalin sheakru 70, da wannan kazamin laifi, wanda dukkanin su suka amsa aikata lafin.

Sai dai wani ma’aikacin kotun, ya shaidawa BBC hausa cewa babu wani lauya da ya wakilci wadanan mutanen a yayin zaman shari’ar, da kotun ta yanke hukunci ranar Laraba,.

Kara karanta wannan

Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

kotun
Kotu ta yanke wa yan luwadi hukuncin kisa a jihar Bauchi
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar Ningi, Adamu Dan Kafi, ya fadawa wa BBC hausa cewa an kama masu laifin ne a kauyen a watan Mayu, suna amfani da kwakakwa da dabino wajen yaudarar kananan yara suna aikata luwadi da su.

Ya kuma kara da cewa masu laifin suna da damar daukaka kara cikin wata daya bayan yanke hukunci

Kano: A wani labarin Kotu Ta Hana Ganduje Ciyo Bashin Naira Biliyan 10 Don Siyo CCTVKyamara

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Abdullahi Liman, a ranar Juma'a ta hana gwamnatin Jihar Kano ciyo bashin Naira biliyan 10 don saka kyamaran tsaro na CCTV da wasu kayan tattara bayanan tsaro, Daily Nigerian ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel