Tambaya zuwa ga masu kalubalantar addu'ar da na yiwa Atiku: Alaramma Ahmad Sulaiman

Tambaya zuwa ga masu kalubalantar addu'ar da na yiwa Atiku: Alaramma Ahmad Sulaiman

  • Alaramma ya yi raddi ga masu sukarsa kan sabuwar addu'ar da ya yiwa Alhaji Atiku Abubakar
  • Malamun addinin ya jera wasu tambayoyi da yake yiwa masu kalubalantarsa kan wannan addu'a da yayi
  • Bidiyon addu'ar da Malam Ahmad Sulaiman ya yiwa Alhaji Atiku Atiku Abubakar ya bar baya da kura

Kano - Shahrarren Alaramma kuma makarancin Al-Qur'ani, Malam Ahmad Sulaiman, ya yi martani ga masu kalubalantarsa kan addu'ar da ya yiwa Alhaji Atiku Abubukar.

Malam Ahmad Sulaiman ya dauki sabuwar bidiyo inda yake yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, addu'ar nasara a zaben 2023.

Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a takarar kujerar shugaban kasa.

Bidiyon addu'ar da Ahmad Sulaiman ya yiwa Atiku ya bar baya da kura.

Alaramma Ahmad Sulaiman
Tambaya zuwa ga masu kalubalantar addu'ar da na yiwa Atiku: Alaramma Ahmad Sulaiman Hoto: Ahmad Sulaiman Ibrahim
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Jerin 'yan takara 14 da suka ki janyewa, ake fafatawa dasu

A martaninsa da yi yiwa take 'Tambaya zuwa ga masu kalubalantata Akan nayiwa Alh Atiku Abubakar Wazirin Adamawa Addu'ar fatan zama Shugaban kasa a 2023' yace:

Laifi ne dan nayiwa musilmi Dan uwana
Addu'a akan Allah yasa Shine Alkhari a 2023?
Lai fine Dan nayimai Addu,a Allah yabashi ikon gyara mana kasar,mu Nigeria?
Laifi ne Dan nayi mai Addu'ar Allah karya barshi da wayonsa yayi riko da hannunsa akan dai dai?
Kuma laifi ne danna nuna Ra,ayina akansa?
A 2015 nayiwa General Mohd Buhari Addu,a me yasa ba'ace komai ba? Har rally naje na buhari
Buhari da Atiku duk musilmai ne yan uwana yan Arewa
Jahilai ne suke ganin wai malami bazai shiga siyasa a dama dashi ba
Kuma dama inza kayiwa mutum Nasiha cewa akayi ka fito in public kana fada?
Ko cewa akayi ka neme shi kaidashi kayi me?

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwani: 'Yan takarar Kudu maso Gabas sun tura wasika ga Buhari kan batun zabo magajinsa

Nima fa Dan kasa ne yarda kakeda yanci nima inada yanci
Daga karshe inawa kasar,mu Addu'a Allah ya bamu kwanciyar Hankali da zama lfy wannan tsadar rayuwa da muke ciki Allah ya kawo mana sauki ya rabbi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel