Buhari ya taso daga Madrid, yana hanyarsa ta dawowa Najeriya

Buhari ya taso daga Madrid, yana hanyarsa ta dawowa Najeriya

  • Shugaban kasar Najeriya ya kammala ziyarar da ya kai kasar Andalus kuma yana hanyarsa ta dawowa Najeriya
  • Buhari ya kwashe kwanaki uku a Andalus yana ganawa da mutane daban-daban ciki har da yan kasuwa
  • Shugaban kasan ya rattafa hannu kan yarjejeniya da dama da zasu gudana tsakanin Najeriya da Andalus

Madrid - Shugaba Muhammadu Buhari ya taso daga babbar birnin kasar Andalus, Madris, kuma yana hanyarsa ta dawowa Najeriya bayan ziyarar kwana uku da ya kai.

Shugaban ya taso daga Torrejon Airbase, Madrid, misalin karfe 8 na safiyar Juma'a, rahoton TheNation.

A kwanaki uku da yayi a Madrid, Buhari ya gana da Shugaban kasar Andalus, Pedro Sanchez da kuma Sarkin kasar King Felipe VI.

Yayin ganawarsa da Shugaba Sanchez; Najeriya da Andalus sun rattafa hannu kan yarjejeniya tara wanda ya hada da yarjejeniyar mikawa juna mai laifi, matsalar rashin tsaro, harkokin al'adu da Kimiya da fasaha.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

Hakazalika ranar Alhamis, ya halarci taron yan kasuwa da yan siyasa da cibiyar kasuwancin Andalus ta shirya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan haka ya gana da yan Najeriya mazauna Andalus, wanda ya hada da yan kwallo da wasu masu zuba jari dake da niyyar zuwa Najeriya.

Buhari ya samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Antoni Janar, Abubakar Malami (SAN); Ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Adeniyi Adebayo; Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed da Ministan harkokin cikin gida, Rauf AregbeSola.

Sauran sun hada da Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare; mataimakin Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora; NSA Babagana Munguno; Shugaban hukumar leken asiri, Amb Ahmed Rufa'i Abubakar da shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel