Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai shilla Madrid, kasar Spain yau Talata

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai shilla Madrid, kasar Spain yau Talata

  • Yan kwanaki bayan dawowa daga Malabo, Shugaba Buhari zai sake tafiya kasar Spain yau Talata
  • Shugaban kasan zai samu rakiyar Ministocinsa bakwai da shugabannin wasu hukumomi uku
  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kwanaki uku kacal zai yi ya dawo gida

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata, 31 ga watan Mayu zai tafi birnin Madrid, kasar Andalus domin ganawa da Shugaban kasar, Pedro Sanchez.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, yace shugaban Spain ne ya gayyaci mai gidansa.

Ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar.

Ya bayyana cewa Buhari za tafi tattauna abubuwa da dama masu muhimmanci kuma zasu rattafa hannu kan wasu yarjejeniya da suka kulla a baya.

Kara karanta wannan

2023: Namadi Sambo, Sule Lamido da wasu jiga-jigan PDP a arewa sun ziyarci Atiku Abubakar

A cewarsa, abubuwan da za'a tattauna kai sun hada da hadin kai wajen kawar da matsalar rashin tsaro, harkokin al'adu, yarjejeniyar mikawa juna mai laifi, dss.

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaba Buhari kasancewarsa shugaban Najeriya na farko da zai kai ziyara kasar, zai gana da Sarkin Spain, King Felipe VI."
"Zai tattauna lamuran hadin kai wajen kasuwanci da hannun jari, makamashi, Sufuri, Kiwon lafiya da cigaban wasanni."
Zai dawo ranar Juma'a, 3 ga Yuni, 2022.

Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Antoni Janar, Abubakar Malami (SAN); Ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Adeniyi Adebayo; Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed da Ministan harkokin cikin gida, Rauf AregbeSola.

Sauran sun hada da Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare; mataimakin Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora; NSA Babagana Munguno; Shugaban hukumar leken asiri, Amb Ahmed Rufa'i Abubakar da shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel