Zagin shugabannin Musulmai da Malamai shima zagin Manzon Allah ne, Dr. Ahmad Gumi

Zagin shugabannin Musulmai da Malamai shima zagin Manzon Allah ne, Dr. Ahmad Gumi

Sheikh Dr Ahmad Mahmoud Gumi. malami ne mazaunin jihar Kaduna kuma mai karantarwa a Masallacin Sultan Bello dake unguwar Sarki.

Ya fitar da jawabi game da maganganun da akeyi kalaman da yayi biyo bayan kisan Deborah Samuel da tayi kalaman batanci da Manzon Allah (S.A.W)

Dr. Ahmad Gumi
Zagin shugabannin Musulmai da Malamai shima zagin Manzon Allah ne, Dr. Ahmad Gumi Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

ZAGIN SHUGABANNIN MUSULMAI DA MALAMAI SHIMA ZAGIN MANZON ALLAH NE!

Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a agareshi yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

روى أَبو هُرَيْرَةَ ، رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ " مَنْ أَطَاعَنِي فَقَدْ أَطَاعَ اللَّهَ ، وَمَنْ عَصَانِي فَقَدْ عَصَى اللَّهَ ، وَمَنْ يُطِعِ الأَمِيرَ فَقَدْ أَطَاعَنِي ، وَمَنْ يَعْصِ الأَمِيرَ فَقَدْ عَصَانِي وَإِنَّمَا الإِمَامُ جُنَّةٌ يُقَاتَلُ مِنْ وَرَائِهِ وَيُتَّقَى بِهِ فَإِنْ أَمَرَ بِتَقْوَى اللهِ وَعَدَلَ فَإِنَّ لَهُ بِذَلِكَ أَجْرًا وَإِنْ قَالَ بِغَيْرِهِ فَإِنَّ عَلَيْهِ مِنْهُ". متفق عليه.

Ma’ana:

Duk wanda yayimun da’a to lalle yayi wa Allah da’a ne. kuma duk wanda ya saba mun ya saba wa Allah ne. Kuma duk wanda yayiwa shugaba da’a lalle yayimun da’ane kuma wanda zai sabawa shugaba to lalle ya saba mun ne. Shifa shugaba ansashi ne kawai domin garkuwa dashi ayi jihadi a bayansa ko ayi kariya da shi. Idan yayi umurni da taqwa kuma yayi adalci to lalle yanada wani lada domin haka in kuma ya aikata sabanin haka to yanada zunubu akansa daga gareshi” Al-buhari Da Muslim suka ruwaito daga Abu Hurairah.

Faidodi:

1. Yin da’a ga shugabanin da musu biyayya wajibi ne kuma saba musu sabawa Manzon Allah ne koda ko su masu laifi ne ko kuskure, sai dai ayi musu nasiha kawai ta tare da zagi ko badanci ba. Allah – subhanahu wa taala- yayi umurni da musu da’a.

2. Zagin su fasikanci ne kuma zagin wanda yace a mutuntasu ne watau Manzon Allah. Kuma Malamai sune magadan annabawa.

3. Baa yin jihadi sai dai bayan shugaba, amma mutane su dauki doka a hannunsu wannan sabawa shugabaninne kuma sabawa manzon Allah ne. Ba jihadi bane kisa ne da bijirewa, aikin Alkhawarijawa.

4. Musulunci ba hauka bane, bin tsari ne da biyayya.

5. Saboda haka kai mai zagin Shugabanni da Malamai kasan matsayinka kada Shedan ya rudaka cikin laifi da zunubi. Kame bakinka or ka fadi alheri.

Allah Ya gyara muna halayen mu ya ilmantar damu ilimi mai ankani. Amin

Asali: Legit.ng

Online view pixel