Yawancin matukan babur na Okada yan ta'adda ne, kwamishanan yan sandan jihar Legas

Yawancin matukan babur na Okada yan ta'adda ne, kwamishanan yan sandan jihar Legas

  • Gwamnatin jihar Legas ta haramta aikin Okada wanda aka fi sani da babur a kananan hukumomi shida a jihar
  • Hukumar yan sandan jihar ta lashi takobin fito na fito da dukkan dan babur din da aka kama yana aiki
  • Kwamishanan yan sandan jihar ya ce mafi akasarin masu aikin babur yan ta'adda ne

Legas - Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya bayyana cewa yawancin matasa masu aikin tuka babur a jihar Legas yan ta'adda ne masu aikata laifuka a fadin jihar.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da haramta tukin babur a kananan hukumomi shida a ranar Laraba.

Yayin hira a shirin Sunrise Daily na tashar ChannelsTV ranar Alhamis, Kwamishanan Alabi ya bayyana cewa an kwace lasisin yan babur da yawa bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Yadda bene mai hawa 3 ya murkushe jama'a, mutum 4 sun rasu, 5 sun jigata

Yace:

"Bari in fayyace, yawancinsu yan ta'adda ne suna basaja da aikin tuka babur."
"Mun damkesu da yawa da bindigogi lokacin ayyukan ta'addancinsu kuma mun gurfanar da su a kotu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Okada
Yawancin yan Okada ya ta'adda ne, kwamishanan yan sandan jihar Legas

Kwamishanan ya kara da cewa kullum ana amfani da wadannan baburan wajen aiwatar da ayyukan alfasha.

A cewarsa:

"Suna amfani da Okada wajen aikata laifuka da dama a unguwanni; shi yasa muke tattaunawa da kungiyoyinsu."
"Hanya mafi kyawu shine korasu gaba daya daga titunanmu saboda basaja suke da aikin babur alhali yan ta'adda ne."

Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya bayyana cewa hukumar za tayi fito-na-fito da yan bakin haure dake zuwa jihar aikin babur.

Alabi ya bayyana hakan ranar Juma'a yayin hira da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Legas.

Kara karanta wannan

Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

Ya ce hukumar na sane da wasu yan bakin haure dake aikin Okada a jihar kuma zasu damke su.

NAN ya ruwaito cewa mafi akasarin masu aiki da babur a Legas ya kasashe mau makwabtaka da Najeriya ne.

Cikinsu akwai yan kasar Nijar, Togo, Kotono da Chadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: