Zamu kara adadin daliban muke ciyarwa kullum da milyan 5, Sadiya

Zamu kara adadin daliban muke ciyarwa kullum da milyan 5, Sadiya

  • Minista Sadiya Farouq ta bayyana cewa ma'aikatarta na shirin kara yawan daliban da za'a rika ciyarwa
  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kulli yaumin tana ciyar da mutum milyan tara kulli yaumin
  • Yanzu an samu umurnin kara sunayen dalibai milyan biyar da za'a fara ciyarwa

Damaturu - Gwamnatin tarayya ta bada umurnin sanya sunan sabbin dalibai milyan biyar cikin wadanda ake baiwa abinci kullum a makarantun gwamnati a fadin tarayya.

Ministar tallafi, walwala da jin dadin jama'a, Hajia Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a Damaturu, jihar Yobe, yayin taron raba kayan girki ga ma'aikatan jihar, rahoton TheNation.

Ministar, wacce ta samu wakilcin mataimakin diraktan Braille Library Bauchi, Hassan Maidugu, ya ce an yi wannan shiri ne don kawar da talauci da inganta rayukan al'umma.

Kara karanta wannan

Tambuwal da 'Yan siyasa 3 da za su shiga zaben 2023 da niyyar takarar kujeru 2 a lokaci 1

Ya kara da cewa kawo yanzu mutum milyan tara ake ciyarwa kuma an dauki sama da masu girki 100,000.

A jihar Yobe kuwa, ya ce daliba 103,929 ake ciyarwa kullu yaumin a kananan hukumomin jihar 17 a makarantu 248.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya samu wakilcin Bulau Aisami Geidam yace gwamnatinsa zata cigaba da baiwa wannan shiri karfin gwiwa.

Zamu kara adadin daliban muke ciyarwa kullum da milyan 5, Sadiya
Zamu kara adadin daliban muke ciyarwa kullum da milyan 5, Sadiya
Asali: Twitter

Gwamnatin Buhari na kashe N10bn a wata wajen ciyar da dalibai, FG

Gwamnatin tarayya na kashe kimanin naira bilyan 10 a wata wajen shirin ciyar da daliban makarantun firamare a fadin tarayya.

Wannan aiki na gudana ne karkashin Ministar tallafi, jin kai, da jin dadin jama'a, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

Jagoran shirin, Dr Umar Bindir, ya bayyana hakan ranar Litinin, a taron warshan masu ruwa da tsaki na kwana biyu kan samar da takardar doka kan shirin, kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito.

Kara karanta wannan

A zauna lafiya: Gamayyar gwamnonin Arewa sun yi Alla-wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi

Dr Bindir ya bayyana cewa akwai muhimmancin a samar da takardar tsari kan shirin ciyar da dalibai don a samu cigaban shirin.

Yace ana ciyar da sama da dalibai milyan 10 a rana kuma N100 aka yi kiyasi kan kowani yaro a rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel