A zauna lafiya: Gamayyar gwamnonin Arewa sun yi Alla-wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi

A zauna lafiya: Gamayyar gwamnonin Arewa sun yi Alla-wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi

  • Gamayyar gwamnonin Arewa sun yi Alla-wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi a jihar Sokoto a makon jiya
  • Kungiyar gwamnonin ta kuma bayyana damuwarta ga wannan lamari, inda ta ce bai kamata al'umma su ke daukar doka a hannu ba
  • Hakazalika, kungiyar ta mika ta'aziyya ga iyalan Deborah da kuma jajantawa gwamnatin jihar Sokoto

Filato - Kungiyar Gwamnonin Arewa ta yi Alla-wadai tare da kira da a kwantar da hankula bayan kisan da aka yi wa wata Deborah Samuel dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, bisa zarginta da yin batanci ga fiyayyen halitta.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dr Makut Maham ya mika a Jos, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

Gwamna Lalong ya magantu a madadin gwamnonin Arewa kan kisan daliba Deborah
Sokoto: Gamayyar gwamnonin Arewa sun yi Alla-wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi | Hoto: preiumtimesng.com
Asali: UGC

Gwamnan ya ce gwamnonin Arewa sun damu matuka tare da yin Alla-wadai da abin da ya faru, kuma hakan abin Alla-wadai ne ganin an dauki doka a hannu.

Gwamnonin sun yi nuni da cewa, duk wani yunkuri na daukar doka a hannu wajen magance matsalar addini ko makamancinsa, na iya haifar da rudani.

Gamayyar gwamnonin ta kuma jajantawa iyalan mamaciyar tare da yin kira da a bar jami’an tsaro su yi bincike sosai kan lamarin.

Ta kuma jajanta wa Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto kan lamarin, tare da yaba wa matakan da ya dauka na maido da zaman lafiya, kamar yadda Independent ta ruwaito.

Gwamnonin sun ba shi tabbacin goyon bayansu da addu’o’insu wajen ganin an shawo kan lamarin, tare da bayyana cewa za su tabbatar da daukar matakan da suka dace domin dakile sake afkuwar irin wannan lamari a ko'ina a yankin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi

Sun kuma jaddada bukatar al’ummar Arewacin kasar nan da ‘yan Najeriya da su rika nuna kauna, hakuri da mutunta juna ba tare da la’akari da addini, kabila ko wata alaka ba.

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

A wani labarin, babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda wata daliba ta shararawa Annabin Allah ashariya a wani faifan sauti da ya yadu a yanar gizo.

A bangare guda, malamin na addinin Islama ya amince da daukar doka a hannu ba daidai bane, amma ya nuna goyon bayansa ga hakan idan dai janibin manzon Allah aka taba.

A wasu rubuce-rubuce da ya yada a shafinsa na Twitter, malamin ya nuna fushi tare shiga tashin hankali bisa jin yadda aka ci mutuncin zababben Allah Annabi Muhammadu SAW.

Asali: Legit.ng

Online view pixel