Da duminsa: An damke tsohon shugaban hukumar rashawa a Kano, Muhyi Rimin Gado

Da duminsa: An damke tsohon shugaban hukumar rashawa a Kano, Muhyi Rimin Gado

  • Yan sanda sun cika hannu da tsohon shugaban hukumar rashawa a Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado
  • Bayan sama da wata guda suna nemansa ruwa a jallo, yan sandan sun gano shi a Abuja unguwar Asokoro
  • Ana zargin Rimin Gado ya aikata wasu laifuka amma ya ki gurfana gaban majalisar dokokin Kano

Abuja - Jami'an hukumar yan sanda sun damke tsohon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa a jihar Kano PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa an damke Rimin Gado ne a masaukin gwamnan jihar Sokoto dake birnin tarayya Abuja.

An tattaro cewa ya je gidan masaukin ne halartan zaman tantance yan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Rahoton ya kara da cewa bayan da aka tantanceshi matsayin mai niyyar takara, yan sandan suka yi awon gaba da shi kuma suka kaisa ofishinsu dake Abuja.

Kara karanta wannan

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Wasu majiyoyi sun ce za'a garzaya da shi Kano don gurfana gaban hukuma.

Zaku tuna cewa a ranar 28 ga Maris, yan sanda sun yi kokarin kama Rimin Gado a gidanshi amma basu samu nasara ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhyi Rimin Gado
Da duminsa: An damke tsohon shugaban hukumar rashawa a Kano, Muhyi Rimin Gado
Asali: Facebook

Laifin me Rimin Gado yayi

A watan Yulin 2021 aka dakatad da Muhyi Magaji daga kujerarsa ta shugaban hukumar yaki da rashawa bayan ya kaddamar da binciken wasu badakalan kwangila da aka baiwa wasu kamfanoni masu alaka da iyalan gwamnan jihar Kano.

Daga baya majalisar dokokin jihar ta bukaci Rimin Gado ya gurfana gabanta don gudanar da bincike kansa amma yaki halarta saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

A sakon da ya aikewa majalisar ya hada da takardar shaidar asibiti na nuna cewa ba shi da lafiya.

Amma ranar 19 ga Yuli, 2021, bisa bukatar majalisar, Asibitin tarayya dake Abuja ya aike wasika majalisar dokokin Kano cewa takardun rashin lafiyar da Rimin Gado ya gabatar na bogi ne.

Kara karanta wannan

Hotunan 'Dawafi na musamman da aka yi don Tinubu a Masallacin Harami, yace a yiwa Najeriya addu'a

A takarda mai lamba NHA/CMAC/GC/0117/2021/V.I/01, diraktan harkokin jinya a asibitin tarayya, Dr. A.A. Umar, yace sun yi bincike kuma sun gano takardun bogi ne.

Muhuyi Rimin Gado ya shigar da Ganduje Kotu

A watan Febrairu, 2022, Muhuyi Rimin-Gado, ya shigar da Ganduje kotun ma'aikata kan korarsa da akayi daga bakin aiki.

Daga cikin wadanda ya shigar karar akwai Antoni Janar na jihar Kano, majalisar dokokin jihar Kano, Akawunta janar na jihar Kano, shugaban hukumar, Mahmud Balarabe, da kwamishanan yan sandan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng