Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

  • Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, ya ayyana shiga tseren kujerar gwamnan jihar Kebbi
  • Ministan wanda ya sanar kudirinsa ranar Alhamis kuma karkashin jam'iyyar All Progreasives Congress (APC)
  • Tun a shekarar 2014, Ministan ya nemi takarar gwamna a APC, amma ya sha kaye a zaɓen fidda gwani

Birnin Kebbi - Ministan shari'a kuma Antoni Janar na ƙasar nan, Abubakar Malami, ya bayyana shirinsa na neman takarar gwamnan Kebbi a babban zaɓen 2023 dake tafe.

TheNation ta rahoto cewa Malami, wanda ya bayyana shirinsa ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, 2022.

Malami yace ya yanke shawarar takara ne bayan amsa kiran da mutane ke masa na ya zama gwamna.

Yanzu-yanzu: Antoni Janar, Abubakar Malami, ya shiga takarar neman gwamnan Kebbi
Yanzu-yanzu: Antoni Janar, Abubakar Malami, ya shiga takarar neman gwamnan Kebbi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

Malami ya bayyana hakan a jawabin da yayi a Birnin Kebbi yayin tattaunawa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC, riwayar Tvcnewsng.

A jawabinsa yace:

"Mutanen jihar ne suka matsa min in nemi gwamna a 2023. Bisa tarbiyyan gidanmu kuma 'dan malamin addini, ba zan nemi wani mukami ba ko in ga kaina na cancanci wani matsayi sai da al'umma sun bukata."
"Na bada gudunmuwa mai yawa ga kasar nan da kuma jihar nan wajen samar da ayyukan yi, yaki da talauci, noma da taimakon mata."

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, a jawabinsa ya yi kira da shugabannin jam'iyyar kada suyi kasa a gwiwa wajen hada kan 'yayan jam'iyya.

Ya yi kira ga matasa su yi koyi da tawali'un Malami a matsayinsa na dan Malamin addini.

Sabuwar dokar APC ta baiwa Amaechi, Ngige awanni 72 su yi murabus ko su hakura da takararsu

Wata sabuwar doka da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka saki a ranar Talata, ta tanadi cewa ya zama dole duk masu mukaman siyasa da ke da niyan shiga zaben fidda gwaninta a dukkan matakai su yi murabus akalla kwanaki 30 kafin zaben.

Bisa ga sabuwar dokar, wasu daga cikin yan majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke neman takarar kamar su ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi da takwaransa na kwadago, Chris Ngige, suna da sauran kwanaki uku kacal su yi murabus ko su hakura da takararsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel