Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya

Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya

  • Bayan sanarwar ganin watar azumin Ramadana mai alfarma, Shugaba Buhari ya taya Musulman Najeriya murna
  • A sakon maraba da Ramadanansa, Shugaban kasan ya yi kira ga Musulmai su ciyar da talakawa abinci
  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad ya sanar da ganin wata da kuma kaddamar watar azumi

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya taya al'ummar Musulman Najeriya murnan ganin watar Ramadana bayan sanarwan Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

A sakon taya murnarsa, shugaba Buhari ya yi kira ga Musulmai su yi amfani da wannan dama wajen ciyar talakawa da marasa galihu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma'a, 1 ga watan Afrilu, 2022.

Buhari ga Musulman Najeriya
Ina muku maraba da watar Ramadana, ku baiwa talakawa abinci: Buhari ga Musulman Najeriya Hoto: Presidency
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari yace lokacin azumi wani dama ne dake nunawa masu hannu da shuni irin yunwan da talaka ke fama da shi kulli yaumin.

Buhari ya shawarci Musulmai su daina asarar abinci da almubazzaranci yayinda wasu ke fama da yunwa da kunci.

Ya yi kira ga Musulmai su rika tunawa da makwabtansu, talakawa da marasa karfi.

An ga watan Azumin Ramadana a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban kwamitin koli na harkokin addinin musulunci, Muhammad Sa'ad Abubakar ya sanar da ranar Asabar 2 ga watan Afrilu wacce ta yi daidai da ranar 1 ga watan Ramadan ta 1443, wacce ke nuna fara azumin watan Ramadan.

Sultan din ya bada wannan sanarwar ne cikin wata sanarwa ta talabijin da kuma Twitter a shafin NSCIA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel