Yanzu-yanzu: An ga watar azumin Ramadana a kasar Saudiyya, gobe za'a tashi da azumi

Yanzu-yanzu: An ga watar azumin Ramadana a kasar Saudiyya, gobe za'a tashi da azumi

  • Gwamnatin Kasar Saudiyya ta sanar da ganin watar Ramadana na bana a wurare daban-daban na kasar
  • Kamar yadda aka saba shekara-shekara, gwamnatin kasar kan sanar da al'umma su fita duban wata
  • Idan an ag watar ranar 29 ga Sha'aban za'a dau azumi, idan ba'a gani ba, sai watar ta cika talatin

An ga azumin watar Ramadana a kasar Saudiyya ranar Juma'a, 1 ga watan Afrilu, 2022,labari da duminsa na nunawa.

Shafin Masallatan Makkah da Madina, Haramain Sharifaini, ya ruwaito cewa an ga watan a wurare daban-daban a fadin kasar.

Saboda haka, za'a fara azumin watar Ramadana ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, 2022.

Tunatarwa: Abubuwan da ya kamata kusani masu muhimmanci kafin fara Azumin Ramadan

Ramadan na ɗaya daga cikin ginshiƙan Addinin Musulunci guda biyar kuma shi ne wata na 9 a cikin jerin watannin Musulunci guda 12.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista - Buhari ga kamfanonin sadarwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Musulmai na farin ciki da watan kasancewar a cikinsa ne aka fara yi wa Annabi Muhammad (SAW) wahayi na farko na littafi Mai tsarki Alƙur'ani.

A wannan watan Musulmai na ƙara gyara halayen su kuma su ƙara matsawa kusa da Ubangijinsu

Suna Azumi ne ta hanyar daina cin abinci da sham abin sha, shan kwayoyi da kuma kame wa daga saduwa da matansu na tsawon kwana 29 ko 30.

Haka nan kuma an so Musulmai su nisanci aikata laifuka kamar maganar wani a bayan idonsa a tsawon watan Ramadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel