Amfani da ayar Qur'ani da Genevieve ta yi a wata wallafa, ya tada hankalin 'yan kudu

Amfani da ayar Qur'ani da Genevieve ta yi a wata wallafa, ya tada hankalin 'yan kudu

  • Wani bidiyo da jarumar Nollywood, Genevieve Nnaji ta wallafa mai dauke da ayar Qurani, darduma da makabarta ya janyo cece-kuce
  • A cikin bidiyon, an yi tunatarwa ne kan cewa duniya duk mafarki ce amma lahira ce matabbata, kuma ayar Qurani ta bayyana cewa kowacce rai sai ta mutu
  • Ganin wannan wallafar ke da wuya mabiyanta na kudanci suka dinga tsokaci tare da zargin cewa ko jarumar ta Musulunta ne ganin tafarkin da ta kama

Wani gajeren bidiyo da jarumar masana'antar kudancin kasar nan ta Nollywood, Genevieve Nnaji ta yi ya tada hankalin 'yan kudu inda ake ta tattaunawa a kafar sada zumuntar zamani tare da musayar ra'ayi.

Gajeren bidiyon ya kunshi tunatarwa ne kan duniyar nan ba komai bace, lahira ita ce madawwama, ya kasance da turanci inda ake nuna abubuwan duniya duk mafarki ne amma na lahira ne tabbatacce.

Kara karanta wannan

Allah ya yarda, Tsohuwar jaruma Saima Muhammad ta amarce

Amfani da ayar Qur'ani da Genevieve ta yi a wata wallafa, ya tada hankalin 'yan kudu
Amfani da ayar Qur'ani da Genevieve ta yi a wata wallafa, ya tada hankalin 'yan kudu. Hoto daga The punch
Asali: Facebook
Bidiyon ya ce: "Don Allah, Don Allah, ku farka, ku farka"

An kara da saka hoton Al-Qur'ani da darduma da makabarta sannan a karshe aka rufe da ayar Qur'ani mai bayyana cewa dukkan rai sai ta dandani dacin mutuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ko da jarumar ta wallafa wannan bidiyon, sai ya zama abun surutu da fargaba daga mabiyanta 'yan kudu kan kar fa a ce jarumar Musulunta take so ta yi ko kuma ta yi, idan ba haka ba ta na Kirista mai ya hada ta da wallafa ayar Qur'ani, darduma da makabarta?

Duk da a bangaren story ta wallafa bidiyon kuma tsarin story na Instagram duk bayan sa'a 24 abinda aka wallafa zai goge.

Sai dai wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumunta mai suna @Poshjournal ta kwafo bidiyon tare da sake wallafa shi a shafinta tare da yin tsokacin cewa Genevieve ta wallafa bidiyon gami da hoton Qur'ani, darduma da makabarta. Allah dai yasa jarumar kalau take.

Kara karanta wannan

Budurwa ta yi watsi da saurayin da ya kashe N1m don tafiyarta UK, ya fada tashin hankali

Mabiyanta sun dinga nuna damuwarsu kan wannan lamarin inda wasu ke zargin cewa Musulunta za ta yi, wasu kuwa suna cewa ai Najeriya kowa yana da 'yancin yin addinin da ya ga dama, babu wani abun tashin hankali idan Musulunta za ta yi. Wasu kuwa gani suke wallafa ce kawai babu wata manufa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel