Babbar magana: Hukuncin kotu kan dokar zabe ta Buhari ya raba kan Sanatoci

Babbar magana: Hukuncin kotu kan dokar zabe ta Buhari ya raba kan Sanatoci

  • Majalisar dattawan Najeriya ta samu rabuwar kai yayin da aka dauko batun dokar zaben ta shugaba Buhari
  • A baya dai wata kotun babban birnin tarayya ta ba da umarni ga gwamnati kan cire wani yankin na dokar zabe
  • Majalisa ta damu, inda wani sanata ya bayyana hadarin da ke tattare da kotu ta kalubalanci matsayin majalisa da ke samar da doka

Legas - Da alamu dai an samu rarrabuwar kawuna a ranar Talata kan kiran da majalisar dattawa ta yi na yin muhawara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na haramta sashe na 84(12) na dokar zabe, The Nation ta ruwaito.

Rikicin dai ya faro ne a lokacin da Sanata George Sekibo daga jihar Ribas, yayin da yake dogaro da doka ta 10 da 11 na majalisar dattawa, inda ya tunawa takwarorinsa yadda ayyuka daban-daban na bangarorin gwamnati guda uku suke.

Majalisa ta dauki dumi
Babbar magana: Hukuncin kotu kan dokar zabe ta Buhari ya raba kan Sanatoci | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kara da cewa hukuncin da kotun ta yanke, wanda ya soke matakin da Majalisar ta dauka, wani mummunan lamari ne da bai kamata a bari ya tafi haka ba.

Ya ce idan har aka bar batun, jam'iyyun siyasa za su iya kalubalantar matsayoyin majalisar a gaban Kotuna.

Sekibo ya bukaci takwarorinsa da su dakatar da sauran ayyukan majalisar na ranan domin zama tare da tafka muhawara kan batun.

“Wannan batu yana da matukar muhimmanci. Wadanda suka je kotu don kalubalantar matakinmu ba su hada da mu a matsayin wadanda ke da sha'awar kan batun ba. Ba mu ma san cewa wani lamari na gaban kotu ba.
“Ba zato ba tsammani, sai aka ce mana an yanke hukunci, nan take Gwamnatin Tarayya ta dauke shi.

"Hakan na da hadari kuma muna bukatar daukar mataki cikin gaggawa. Wannan na da mahimmanci don daidaita irin wadannan abubuwan."

Sai dai majalisar ta dattijai ta dage muhawarar kan lamarin zuwa ranar Laraba bayan ra'ayoyi mabanbanta kan wannan hukunci.

Legit.ng Hausa ta tuntuni wani masanin shari'a a Najeriya, Isa Usman esq. wanda ya yi sharhi kan kai ruwa rana da ake tsakanin majalisa da kotu.

Ya bayyana cewa:

"Ba a kotu a kawo doka a kasa ba, a majalisa ake samar da wata doka. Kundin zabe kuma wani shashe ne daga kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka, idan za a amince ko cire sashe na 84(12) a dokar zabe, to dole ne a duba; dokar ta yi daidai da tanadin kundin tsarin kasa? Idan bata yi ba, kuma akwai bukatar dokar, to akwai bukatar majalisa ta sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya domin yin kwaskwarima saboda dokar nan ta zabe ta samu shiga.

"Wannan kenan a fahimta ta, da kuma karatu na."

Kotu ta umarci AGF ya cire sashen da Buhari ya nema a cire daga dokar zabe

A baya kunji cewa, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Umuahia, babban birnin jihar Abia a ranar Juma’a, 18 ga watan Maris, ta umurci ministan shari'a, Abubakar Malami, da ya shafe sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.

Channels Tv ta rawaito cewa, umarnin kotun ya biyo bayan bukatar da shugaban Buhari ya mika wa majalisar dokokin kasar na a soke wani bangare na dokar da ta haramta wa mambobin majalisar zartaswa tsayawa takara ba tare da yin murabus ba.

A hukuncin da ta yanke, babbar kotun ta bayyana cewa ana bukatar masu rike da mukaman siyasa su yi murabus daga mukamansu ne kawai kwanaki 30 kafin zabe ba da wuri ba kamar yadda sashe na 84(12) na dokar zabe ya tanada.

Nduka Edede, wani mai kada kuri'a a jihar Abia kuma mamba a jam'iyyar Action Alliance (AA) ne ya shigar karar gaban kotun.

Jam’iyyar ta AA na daya daga cikin jam’iyyun siyasa da suka kalubalanci AGF kan wannan bangare na dokar zabe.

An yi gaba an dawo baya: Buhari ya nemi a soke wani sashe na sabuwar dokar zabe da ya sanyawa hannu

A tun farko, a ranar Talata 1 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dokokin kasar Najeriya da ta yi wa sabuwar dokar zabe ta 2022 da aka sanya wa hannu kwaskwarima.

A wata wasika daga fadar shugaban kasa da shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan ya karanta yau Talata, shugaba Buhari ya shaidawa majalisar dokokin kasar da ta duba batun cire sashe na 84 (12) gaba daya.

Wannan bangare na dokar zabe ya tanadi doka kan masu rike da mukaman siyasa da su yi murabus daga ofishinsu kafin su yi takarar fidda gwani a jam’iyyunsu na siyasa, inji rahoton Punch.

s

Asali: Legit.ng

Online view pixel